Hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 14.89 a cikin watan Nuwambar shekarar 2020, fiye da na kashi 14.23 wanda aka samu a watan Oktobar shekarar 2020. Masana sun bayyana cewa, wannan karuwear hauhawar farashin da ake samu ya samo asali ne sakamakon rufe iyakokin kasar nan. Rahoton farashin kayayyaki wanda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a ranar Talata, ya nuna cewa kayayyakin abinci ya karu da kashi 18.30 a cikin watan Nuwambar shekarar 2020, idan aka kwatantashi da na kashi 17.38 wanda aka samu a watan Oktoban shekarar 2020.
“Farashin kayayyakin da suka karu sun hada da biredi da hatsi da taankali da doya da alkama da kifi da kayayyaki itatuwa da kayayyakin lambu da man girke-girke.”
A hannu daya kuma, dukkan wani kayayyaki wanda ba na noma ba ya ragu da kashi 11.05 a watan Nuwambar shekarar 2020, idan aka kwatanta da na kashi 11.14 wanda aka samu a watan Oktobar shekarar 2020.
Wasu masana masu suna Mosope Arubayi da Ibukun Omoyeni a nasu ra’ayin suna ganin cewa, an fara samun hauhawar farashin kayayyaki ne tun a shekarar 2016, wanda a duk watan 12 sai an samu karin da ba a taba samu ba.
Sun kara da cewa, idan ba a daauki matakan da suka dace ba kafin karshen wannan shekara, to haka za a ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar nan.
A kwanakin nan ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yuwuwar bude iyakokin kasar nan.
Masana sun ci gaba da cewa, idan aka samu jinkirin samar da kayayyakin abinci a shekarar 2021, to ba za a samu wani canji a kan yadda ake gani ba a wannan shekara, yana da matukar mahimmanci a bude iyakokin kasar nan kafin shekarar nan ta kare.