Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Lmapard, ya bayyana cewa zai cigaba da amfani da matasan ‘yan wasa a kungiyar tasa duk da cewa yanzu zasu sayi ‘yan wasa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta watan Janairu.
Lampard ya bayyana hakane bayan da aka tashi daga wasan da Chelsea ta tsallake rijiya da baya, ta kai matakin gaba na kungiyoyi 16 a gasar Zakarun Turai, bayan da ta tsira a hannun Lille da ci 2-1, a gidanta na Stamford Bridge.
Kungiyar ta mamaye wasan a kusan gaba dayan lokacin, inda ta samu nasarar da take matukar bukata daga kwallayen da Tammy Abraham and Cesar Azpilicueta suka ci mata a kashin farko na wasan.
Abraham mai shekara 22, shi ne ya fara zura kwallo a raga da kwallonsa ta 13 a kakar bana bayan minti 19 da shiga fili, bayan da Willian ya cilla masa wata kwallo kuma wannan kwallo da Abraham ya ci ta sa ya zama dan wasan Ingila na farko da ya taba ci wa Chelsea kwallo 13 a gasa a kaka daya kacal, tun bayan Lampard da ya ci mata 17 a kakar wasa ta 2012-13 kuma Abraham din yana da damar wuce Lampard a wannan bajinta, kasancewar a yanzu ko rabin kakar ba a yi ba.
“Zan cigaba da amfani da matasan ‘yan wasan da nake dasu saboda dasu muka fara hakan yana nufin bazan iya daina amfani dasu ba saboda nan gaba sune zasu kasance jagororin wannan kungiyar tamu” in ji Lampard
Bayan kammala wasan rukunin nasu na 8, (Group H), Balencia wadda ta bi Ajad har gida ta doke ta 1-0, tana da maki 11 da yawan kwallo 2, Chelsea na bi mata baya ita ma da maki 11 da yawan kwallo 2.
Ajad, wadda ta ga samu ta ga rashi ta yi waje a matsayi na uku da maki 10 da yawan kwallo shida, yayin da Lille ta kasance ta karshe da maki daya da bashin kwallo 10 kuma za a fitar da jadawalin wasannin mataki na gaba na gasar ta Zakarun Turai, a ranar Litinin, a birnin Nyon, na Switzerland da karfe 12:00 na rana agogon Nijeriya.
Tarihin da aka kafa a wasan Chelsea Da Lille
Da wannan nasara da Chelsea ta samu, Lampard ya zama kociya dan Ingila na farko da ya kai wata kungiya matakin gaba na sili-daya-kwale na gasar ta Zakarun Turai, bayan da ya karbi jan ragamar dukkanin wasanni shida na rukuni na kungiyar, tun bayan da Harry Redknapp ya yi wannan bajinta da Tottenham a kakar wasa ta shekara ta 2010 zuwa 2011.
Maki daya kawai Lille ta samu a wannan kaka da ta zamar mata mafi muni a matakin rukuni na gasar ta cin Kofin Zakarun Turai na Champions League sannan kungiyar ta Lille ta yi wasa shida a gidan kungiyoyin Ingila a manyan gasar Turai kuma ba ta taba yin nasara a ko da daya ba.
Loic Remy ya zama dan wasa na bakwai da ya ci wa Chelsea kwallo kuma ya ci kungiyar a filinta na Stamford Bridge a gasar ta Zakarun Turai ta Champions League, bayan Samuel Eto’o da Fernando Torres da Diego Costa da Michael Ballack da Dabid Luiz da kuma Willian.