Zubairu M Lawal" />

Duk Dalibin Da Ya Ki Bin Dokar Korona Ba Zai Shiga Makarantarmu Ba – IMAPOLY

IMAPOLY

Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Isa Mustapha Agwai da ke garin Jihar Nasarawa (IMAPOLY), Dakta Jostina Anjiode Kotso, ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a ofishinta.

Ta ce, Gwamnatin Jihar Nasarawa da hukumar makaranta sun yi iya kokarinsu wajen dakile duk hanyoyin kauce wa yaduwar annobar cutar Korona a ciki da wajen makarantar.

Saboda gwamnati ta yi feshin maganin kashe cutar Korona kota ina cikin makarantar domin kare lafiyan Dalubai. Kuma hukumar makarantar ta samar da wadacecen abubuwan kare yaduwar cutar.

An samar da robobin ruwa na wanke hannaye da sabulan da man shafawa a hannaye ciki da wajen makarantar duk an ajiye wannan.

Abin da ya ragewa Dalubai shine kowa ya kiyaye wannan dokar babu wani dalubi da zai shiga cikin makarantar ko malami face yayi amfani da Takunkumin rufe fuska kuma ya bi dokoki wajen wanke hannaye da shafa mai.

Tun daga Babban kofar shiga makarantar zuwa kofofin ajujuwan makarantar da ofishoshin malamani akwai wadannan abubuwan da na lisafa dole a keyaye dokokin yaki da yaduwar annobar cutar Korona bairus cikin wannan makaranta.

Duk dalubin da bai sanya Takunkumin ba sai dai ya koma gida ba zai shiga cikin makarantar ba .

Dakta Jostina Anjiode ta ce akwai tsare-tsaren da suke kokarin kawowa masamman a fannin ilimin Na’urar zamani. Su na kokarin samar da cibiyar nazarin Kimiyyar Zamani ta Hanyar ICT.

Ta kuma gargadi dalibai da ke shigowa makarantar daga cikin Jihar da wasu jihohin da su tabbatar karatu shine zai kawo su, domin yanzu hukumar makarantar Isa Mustapha Agwai ba za ta amince da wasu kungiyoyi na bata tarbiya ko kungiyar asiri ko makamancin wannan ba.

Duk wanda aka kama shi cikin daya daga wadannan kungiyoyin hukumar makarantar Isa Mustapha Agwai( IMAPOLY) zata hukunta shi hukunci mai tsanani. Domin Gwamnatin jihar Nasarawa tana yaki da bata gari da masu aikata miyagun laifuka.

Gwamna Abdullah Sule na Jihar Nasarawa ya tabbatar da cigaban matasa masamman a harkan ilumi mai zurfi. Kuma jihar Nasarawa tana maraba da duk wani bako ko bakuwa amma ba za ta amince da gurbatattun mutani masu shigowa da kungiyoyin asiri ko miyagun laifuka ba.

Dakta Jostina Anjiode Kotso tayi godiya ga Hukumar makarantar da Malaman makarantar dama dalubai da suka baiwa sabobin dokokin hadin kai domin cigaban Jihar Nasarawa.

Exit mobile version