Connect with us

SIYASA

Duk Dan Mazabar Dogara Da Ke Kushesa Butuli Ne, Inji Kungiyar Databo

Published

on

Tun bayan takun sakar da aka samu a tsakanin ‘yan majalisu da shugaban kasar Nijeriya a kwanakin baya.
Wasu bangare sun samu damar yin hujumi sosai a kan Kakakin Majalisar Tarayya, Barista Yakubu Dogara, inda magoya bayansa suka yi zargin cewar wasu marasa kishi da son bata masa suna wanda suka yi zargin cewar daukan nauyinsu ake yi don cimma wata manufa ta daban sun samu damar yin amfani da wancan matsalar wajen neman bata wa Dogara suna.
A bisa haka ne, hadakar kungiyoyi sha biyu 12 daga kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da Bogoro inda nan ne mazabar Kakakin majalisar suka fito hade da taka burgi wa masu neman bacal.
Hadakar Kungiyoyin, wanda suka hadu karkashin lemar kungiyar dattawa da matasan yankunan mai suna Youths and elder’s forum (DATABO) sun shaida cewar babu wani dan mazabar Dogara na hakika da zai amince ya amshi kwangilar bata wa Dogara suna, suna masu kafa hujja da yadda yankunan suke matukar cin gajiyar Yakubu Dogara.
Kungiyar wacce take shaida hakan a zantawarta da ‘yan jarida bayan wani gangamin nuna goyan baya da suka yi wa Kakakin Majalisar, Dogara a mazabarsa ta Tafawa Balewa.
Da yake magana, shugaban kungiyar Alhaji Salisu Musa ya bayyana cewar gangamin sun shirya ne domin karyata shaci-fadin da wasu da suka kira kansu shugabanin APC a kananan hukumomin da Dogaran ya fito, hade kuma da wani wanda ya kira kansa da sunan dan yankin ne wanda basu sanshi ba.
Ya ce, sun yi zargin wai Dogara na yunkurin tsige shugaban kasa Buhari, inda suka bayyana cewar sam babu kanshin gaskiyar cewar Dogara na fada da Buhari, suna masu shaida cewar, “Dogara ce wa mana ya yi, duk wanda ya san ba zai zabi Buhari ba kada ya zabesa. Don me yau wasu za su samu zarafi suna amfani da wani abun da suka jahilcesa wajen neman bata wa Dogara suna a idon duniya? Wannan ba daidai bane, kuma mu masoya Dogara ne za mu kare masa hakkinsa a ko’ina,” In ji shugaban.
“Irin gudunmawar da Dogara ya taka wajen cin nasarar Buhari bai kamata wasu su fage da guzuma suna harbin harsana ba. Dogaran nan fa yana daga cikin ‘Agents’ na Buhari a lokacin zaben fidda gwani,” A cewar shi.
Shi ma da yake tasa bayanin, Mr Bulus Ishaku wanda mamba ne a tafiyar, ya shaida cewar babu wani dan halas da zai kushe aiyukan da Kakakin Majalisar ya yi musu, inda ya bayyana cewar bisa amanarsa ne ma ya sanya suka sanya masa suna da ‘Dan Amana’, ya ce har gobe sun gamsu da yadda Dogara ke gudanar da al’umuransa kuma sun amince su ci gaba da mara masa baya duk inda ya sanya wa gaba.
Ya ce, a dukkanin kananan hukumomi uku da Dogara ke wakiltar, babu wata karamar hukumar da bata samu dumbin aiyuka a cikinta ba, yana mai shaida cewar aiyukan ci gaba da Dogara ya samar basu misaltuwa, ya bayyana cewar ya samar titi mai nisan kilomita 57 a Dass, haka kuma ya dauki nauyin matasa da mata da daman gaske wajen koyar da su noma ta fasahar zamani, kana Dogara ya dauki nauyin mata dubu inda ya basu naira dubu dari-dari domin kama jari, sannan kuma ya gyara makarantun firamare, gina dakunan binciken ilimi a kowace mazabarsa ta Dass, T/Balewa da kuma Bogoro.
Ya ci gaba da shaida aiyukan Dogara, “bayan titin da Dogara ke yi a Dass a cikin Tafawa Balewa ga hanyoyi da daman gaske da ya samar mana, bayan nan ya zo ya dauki nauyin mutane 10,000 daga mazabarsa inda suke koyon kiwon zamani da noman rani a kwalejin ilimi ta Dadin Kowa da ke Gombe, da dai sauran ababen da Dogara ya samar mana,” don haka ne ya bayyana cewar ba za su yi sake da damarsu ba, suna masu sake mara masa baya ya ci gaba da samar musu da ababen more rayuwa.
Shi kuwa Ayuba M. Landi ya shaida cewar an dauki kwangilar wani mai suna Kacalla domin aza wani tubali matsala, “Mu a duk fadin Tafawa Balewa, Dass Bogoro ba mu da wani mai suna Kacallah ballanta na fito yau ya ce sune masu ruwa da tsaki a wannan yankin da har zai ce wai kada Dogara ya sake fitowa takara, wai sun fito da wani mutu. Mu ba mu da wani da ya wuce mana Dogara, shine gatanmu,”
“Dogara har coci-coci ya bi mu yana shaida mana cewar duk wanda ba zai zabi Buhari ba kada ya kuskura ya zabeshi. Yau an zo an fara neman fakewa da wani zance ana cewa wai Dogara yana fada da Buhari, wannan abun kunya ne, kowa ya san irin gudunmawar Dogara. Su masu wannan kwangilar kwadayi ne ya yi musu yawa, babu wani dan Dass, T/Balewa ko Bogoro da zai kalli idon Dogara ya kalli dumbin aiyukan da ya shimfida mana ya ce wai baya tare das hi ai sai butulu,” In ji shi.
Obi Mai Katako wanda ake kira da O & O cewa yake “tun 1985 na zo T/Balewa, tun da na zo na karanci yadda Dogara ke tafiyar da jama’ansa. Ni abun da zan ce, mu dai kabilun da muke rayuwa a wannan mazabar duk wanda ke inkari a kan Dogara ta zo ya zaga ya ga irin aiyukan da Dogara ya yi mana. Don haka babu wanda zai taba sa mu barshi kowaye. Duk wanda ya ce ga wani da fi Dogara ya jira ranar zabe ya zabi wani ya gani, mu kuma mu zabi Dogara a gani,” Kamar yadda ya shaida.
Kungiyar dai ta bayyana cewar Yakubu Dogara bai shirya wata abar da ka iya kawo wa Nijeriya ci baya, suna masu bayyana cewar a kowani lokaci burinsa ya ga jama’an kasar nan sun samu cin gajiyar ribar Domokradiyya, a bisa haka ne ma suka bayyana goyon bayansu dari bisa dari wa Kakakin majlisar ta tarayya, suna masu nemansa da ya daura daga inda yake kai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: