Ibrahim Muhammad" />

Duk Mai Kishin Kano Zai Murna Da Nasarar Gwamna Ganduje – Dantata

Shugaban karamar hukumar birnin Kano. Hon. Alhaji Sabo Muhammad Dantata, ya bayyana nasarar Gwamnan jihar Kano a kotun koli da cewa nasarace ta dorewar cigaban bunkasar jihar Kano.

Ya ce duk mai kishi dason cigaban jihar Kano wajibine yayi farin-ciki yaji  dadin yanda yanda wannan hukunci ya kasance na tabbatarwa Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje zabenda al’umma sukayi masa.

Alhaji Sabo Dantata  ya kara da cewa  ba wani dan jihar  da yake son cigabanta da zaiso ace irin dinbin ayyuka na cigaba  da aketa gudanarwa  karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ya sami tsaiko hakan nema tasa al’ummar jihar Kano suka sake zabarsa  a karo na biyu dan dorewa akai amma wasu yan  hamayya keta kokarin su dawo da hannun agogo baya amma cikin ikon Allah da jajircewa da al’umnar Kano sukayi an tabbatarda Gwamna Allah ya bashi nasara bayan hukumar zabe  ta tabbatar musu da nasara  akaje kotun  zabe ta sake tabbatar masa  haka ma a kotun daukaka kara yanzu kuma a karshe  kotun koli ta tabbatar da cewa shine zabin al’ummar Kanawa.

Hon.Alhaji Sabo Dantata ya ce abinda al’ummar kano zasuyi su taimaki kansu  su kuma taimaki Gwamna Ganduje shi ne su cigaba da bashi goyon baya dayi masa kyakkyawan fata da addu’a  ta Allah ya tsareshi ya bashi kwarin gwiwa ta cigaba da gudanarda ayyukan alkhairi ga jihar kano da al’ummarta.

Exit mobile version