Duk Mai Neman Maganin Talauci Ya Rungumi Kasuwanci – Alhaji Mai Dubji

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Daya daga cikin dattawan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Muhammad Abdullahi Mai Dubji ya bayyana cewa duk mutumin da yake so ya samu maganin talauci a rayuwarsa, ya rungumi kasuwanci.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a Kano.
Da yake tsokaci a kan muhimmanci bunkasa kasuwanci, ya bayyana cewa yanzu dai ko hasidin iza hasada ya gamsu tare da amincewa gine-ginen shaguna da wuraren gudanar da harkokin kasuwanci da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke ta shimfida wa Kanawa ya zama alhairin da za a jima ana tuna shi dasu.

Mai Dubji ya yaba da manyan gine-ginen shaguna da wuraren kasuwanci da ahalin yanzu dubun dubatar matasa ke samun hanyoyin dogaro da kai tare da samun abin sawa abakin salati.
Alhaji Mai Dubji ya ci gaba da cewa wadannan gine-gine da Khadimul Islam ke kwararawa a Kano ya taimaka kwarai da gaske wajen jawo masu sha’awar zuba jari a harkokin kasuwanci ci gaba kwararowa Jihar Kano.

Yace mayan da tsoffin gidajen tsohuwar kasuwar kantin kwari zuwa sabbi irin na zamani, ya baiwa matasa maza da mata samun ayyukanyi, kuma kamar yadda aka sani wadannan gidajen duk mallakar Jama’a ne, yanzu kamfanoni suka sabunta gininsu tare da sayarwa masu bukata.

Kamar yadda aka sani, babban burin Gwamnatin Jihar Kano shi ne bunkasa Kasuwanci sannan da kyakkyawan fatan da Gwamna Ganduje yake dashi na ganin ‘yan kasuwa sun mallaki wadannan wuraren a Jihar Kano.

A karshe Alhaji Muhammad Abdullahi Mai Dubji ya jinjinawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje bisa kyakkyawar manufarta na Inganta harkokin kasuwanc, Wanda haka ke kara tabbatarwa da Jihar matsayinta na cibiyar ciniki a fadin afrika.

Exit mobile version