Munkaila Abdullah" />

Duk Masu Kaurace Wa Al’umma Bayan An Zabe Su, Za Su Gani A Kwaryarsu –Mustapha Lamido

Mustapha Sule Lamido Shi ne dantakar Sanata mai wakiltar Jigawa ta tsakiya karkashin tutar jam’iyyar PDP, cikin tattaunawarsu da wakilinmu Munkaila Abdullah ya bayyana cewa kara wa’adin zabe na sati guda ba zai hana shi yin nasara, ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Menene ra’ayinka dangane da kara wa’adin zabe na sati daya?
Da farko babu ko shakka hukumar zabe ta kasa INEC ta shammaci ‘yan Najeriya. Kuma wannan abun kunya ne abun takaici, kuma ya kamata su sani cewa, duniya tana kallonmu kuma ana kallon abun kunyar da suka aikata don haka ba iyaka kansu suka kunyata ba illa al’ummar Najeriya da kasa baki daya.
Kuma ba ma mu ‘yan jam’iyyun adawa ba, hatta shikansa shugaba Buhari da kansa ya bayyana damuwarsa‎ kan wannan al’amari, kuma duk wani dan kishin kasa musamman yadda akewa Najeriyakallon uwa a Afrika, ba zai ji dadin wannan al’amari ba.
Don haka ya kamata hukumar zabe ta kasa INEC ta guji irin wannan abun kunya dubu da yadda hakan ta faru‎ a kakar zabe ta shekarar 2011 da 2015 yanzu kuma gashi ta kuma faruwa, musamman duba da yadda duk wani bakin mutum a duniya ko wata kasa ta bakake kewa Nijeriya kallon uwa ko jagora, babu ko shakka wannan abun kunya ne kuma muna fata zasu kiyaye faruwar hakan a nan gaba.
Sannan kuma ina kira ga duk wani dan Nijeriya musamman ‘ya’yan jam’iyyarmu ta PDP da su dauki wannan al’amari a matsayin kaddarawa ta Allah kuma su fito a ranar Asabar domin tabbatar da nasarar ‘yan takarkarunmu na PDP a kowanne mataki domin ceto wannan kasa daga halin da ta tsinci kanta.

Ta yaya kake ganin dake wannan zabe ya shafi ‘yan takarkaru?
Babu ko shakka ba iya ‘yan takarkaru ba, hatta ma kungiyoyin sanya idanu na cikin gida da wajen kasar nan da sauran al’umma baki daya ba zasu ji dadin wannan al’amari ba, domin kuwa al’amari wadda aka debawa hukumar zabe tsahon shekaru hudu ta shirya amma bata sanarda dage zabe ‎ba sai da aka zo saura kasa da awonni hudu da fara zabe wannan ba dai dai bane.
Domin duk wani dan kasa wadda yake da ‘yancin jefa kuri’a ya baro wajen aikinsa ya taho gida domen yayi zabe daga baya kuma kace ka dage zaben sai bayan sati daya kaga dole ko dai mutum yayi asarar wannan sati ya zauna a gida ya jira ko kuma ya sake kashe kudi ya koma wajen aiki sannan ya dawo daga baya.
Sannan su kansu ‘yan takara sun riga sun rufe yakin neman zabe wasu ma sun gama duk ganawar da za su yi wakilansu a matakai daban-daban, to kaga dole ne suma su sake sabon lale wadda yin hakan ba shi aka so ba sai dai kawai muce Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tareda mu da kuma al’ummar kasa baki daya.

Duba da cewa abokin takararka na jam’iyyar APC shi ne kan wannan kujera da kake nema, baka ganin cewa wannan zai iya zamar maka wata bazara musamman ma da aka dage wannan zabe?
Ko daya dage wannan zabe ba zai sanya mu kayar da abokanan takararmu ba musamman ma jam’iyya mai mulki ta APC, domin ba wai mune muke bukatar a sauya ba, a’a al’ummar da suka tura shi su ne suka ce sun gaji ya dawo, kuma dole ya dawo domin shi ma wani ne ya sauka shi ma ya hau, wannan ita ce dimokradiyya.
Sannan ina so kuje duk yankuna da karkarunmu ku duba ka gani wa al’umma musamman matasa mata da maza wadanda sune kashin bayan kowacce al’umma, wa suke goyon baya, daga nan ne za ku yarda da cewa dage zabe ba zai taba hanamu kayar da jam’iyyar APC a dukkan matakan zabe ba.
Haka kuma inaso kusan cewa, yanzu kan al’ummarmu musamman matasa ya waye, matukar suka zabe ka to idanuwansu na kanka wajen me kayi musu a wakilcin da suka turaka, ka yi ko baka yi ba? Wannan shi ne ma’auni yanzu bawai kudinka ba, don haka matukar ka gujewa al’ummarka sai bayan shekaru hudu sannan ka dawo kana kara nemam kuri’arsu to za ka gani a kwaryarka. Don haka al’ummar yankina da ma jihar Jigawa baki daya sun ga irin ayyukan alherin da jam’iyyata ta PDP ta gudanar a wannan jiha lokacin tana kan karagar mulki, kuma sun ga abun da jam’iyyar APC ta yi musu kuma za su yanke hukunci da kansu domin ‘yancinsu ne kuma damarsu ce.

Wadanne abubuwa ne sababbi da za ka maida hankali a kansu idan ka yi nasara wanda kake ganin shi wanda yake kai ya kasa yi?
To da farko dai kamar yadda na sha fadi a baya cewa, kujerar Sanata kujera ce wadda ayyukanta suka fi karfi ga samar da doka da dokoki, don haka idan har Allah ya bamu nasara to zan maida hankali waje bujuro da dokoki wadanda za su bunkasa rayuwar matasa da mata tareda jajircewa wajen tabbatarsu domin al’ummarmu.
Haka kuma kamar yadda muka ga jam’iyyar ta PDP ta yi lokacin tana kan karagar mulki a baya wajen bujuro da ayyukan raya kasa, to za mu yi iya bakin kokarinmu wajen tsayawa tsayin daka domin kwato duk wani hakkunan al’ummarmu daga matakin gwamnatin tarayya domin su ma su amfana da dai sauran muhimman ayyuka wadda lokaci ba zai bamu damar ambatarsu ba.

Mene ne kiranka ga al’umma kan wannan zabe da za’a gudanar a gobe Asabar?
Kira ga al’umma shi ne, a yi hakuri da wannan abu da ya faru na daga zabe sannan mu yi ta addu’ar Allah yasa haka ne mafi alkhairi a tare da mu, haka kuma mu fito ranar Asabar matanmu da maza domin kada wa jam’iyyar PDP kuru’u a kowanne mataki domin ceto wannan kasa daga halin da ta tsinci kanta ciki a wannan lokaci, na gode.

Exit mobile version