• Fim Din ‘Zo Mu Zauna’ Ya Kara Saka Min Kauna Da Girmama Ali Nuhu
• Da Fim Din ‘Fil’azal’ Na Samu Kyautar Kujerar Umarah Ta Farko
Shahararriyar jarumar nan da ta jima tauraruwarta na haskawa a Masana’antar Fina-finan Hausa ta ‘Kannyood’ Ummi Nuhu, wadda aka fi sani da Ummi Al’amari ta ce, duk sana’ar da za ta yi a duniya, ba ta fi sana’ar fim kima a wajenta ba. Bugu da kari, ta bayyana wa masu karatu wani sirri na fim din da ta yi mai suna ‘Zo Mu Zauna’, wadda abin mamaki ta ce tana da karaya dai-dai har guda hudu a kafarta lokacin da ake daukar shirin fim din. Har ila yau, ta baiwa jaruman da ke ganiyarsu a halin yanzu shawarwari irin nasu na tsohuwar zuma. Ummi Nuhu ta yi wadannan bayanai ne cikin tattaunawarta da Filin Taurarin Nishadi na LEADERSHIP A YAU JUMA’A tare da wakiliyarmu JUMMAI IBRAHIM, ga yadda hirar ta kasance:
Muna so ki ba mu cikakken sunanki da takaitaccen tarihin rayuwarki?
Assalamu alaikum masu karatu, to da farko ni dai sunana Ummi Nuhu, haifaffiyar Kaduna ce ni. Na yi makarantar Firamare da ta Sikandire duk kaduna, amma asali na ‘yar Kano ce a Karamar Hukumar Bunkure. Daga nan Bunkuren na koma Kano, na fara sana’ar fim. Amma ba wai na koma Kano gaba daya ba ne, na kan zo na koma Kaduna, don a lokacin gaskiya fina-finaina sun fi yawa a Kano shi ya sa sai na zo na fi zama a Kano sosai.
Me ya ja ra’ayinki kika shiga harkan Fim kuma da wane Fim kika fara?
E toh, abin da ya sa na fara fim, da farko dai Fati Mohammed kawar Anty na ce a gidanmu na santa sosai ita da Ali Nuhu har suka zama kawayena sosai. Da farko an taba mun wasa a kan na yi fim sai na ce kai ba zan iya ba. Daga baya kuma sai abin ya fara ban sha’awa har lokacin da wani Garba Babangida kanin Tijjani Babangida ya zo zai shirya wani fim mai suna ‘Al’amari’ kamar wasa na ce zan yi lokacin kusan unguwarmu daya da su, ni ina Sardauna Crescent, su kuma suna Wushishi Road, da haka na fara fim.
A cikin jerin fina-finan da kika yi wanne ne ya fi burge ki kuma me ye dalilinki?
To ni dai duk fina-finaina suna birge ni sosai, amma kuma dole ne mutum yana da wanda ya fi ma sa. Sai dai Kuma gaskiya ina son fim dina guda uku. Na farko dai shi ne al’amari, wanda ba zan taba iya manta shi ba har abada, domin kuwa da shi na fara duk wanda ya sanni a fim dalilin al’amari ne. Sai kuma Fil’azal’ wai kin san shi fil’azal shi ne fim na farko da ya nuna sunan da aka sanni sosai a duniya, kuma na samu alheri sosai dalilin sa, na san mutanan da har yanzu muna tare da wasu cikin aminci da kyautatawa. Kuma dalilin fil’azal ne aka fara ba ni kyautar kujerar Ummarah ta ta farko, da kuma dai dalilai masu yawa wadanda suka shafi rayuwata da ba zan iya bayyana su ba, kuma don Allah kada ki tambaye ni dalili. Sai kuma Fin din ‘Umarni’ ina son umarni saboda labarin, da kuma yadda mutane suka so ni sosai a cikinsa, sannan kuma labarin ya yi min kama da wani labari da ya faru a gaske. Wadannan fina-finan nawa suna birge ni sosai wallahi
To wane fim ne ya fi ba ki wahala wurin dauka kuma me ya sa?
Fim din da ya fi ba ni wahala wajen dauka shi ne ‘Da’ira’ domin kuwa matsayi uku na buga a ciki, kuma ni kadai ce mace a fim din kaf, sai dai wata waka da muka yi a ciki shi ne kawai mata sukai min amshi . Sai kuma ‘Zo Mu zauna’, shi kuma abin da ya sa ya ban wuya shi ne, domin lokacin na karye don ko tafiya ba na iya yi, shi kansa mai ba da umarnin na fim din ya dan sha wuya wajen daukar gurina, domin lallaba ni yake yi don kar na samu matsala. Amma ina son fim din sosai. ‘Zo Mu Zauna’ shi ne ya kara saka min kauna da gimama Ali Nuhu don a lokacin ina tunanin ba zan kara wani amfani ba domin na yi karaya hudu a kafa daya, amma duk da haka Ali ya yi min wannan fim a yadda nake daga na san cewa ba zan iya yi ba.
Ummi kin bace a fim masoyanki da dama suna ta ina ummi, yanzu muna so ki fada masu da kanki?
Gaskiya na bace kam, to kin san yadda rayuwa take, kuma komai da lokacinsa ina nan abuna kawai dai don na daina fitowa a fim ne yanzu shi ya sa, amma Alhamdulillah ina cikin koshin lafiya, kuma za ku ganni kwanan nan insha Allah na gode da kauna, sannan kuma ina so ku sani cewa ina son ku fiye da tunani don ku ne ma har yanzu tauraruwata ke haskawa, na gode sosai.
To Yanzu ya labarin aure yaushe zaki gayyacemu mu sha biki?
Nan ba da dadewa ba insha Allah
Shin ko nan gaba bayan kin yi aure kina da sha’awar zama mai ba da umurni ko mai shirya fim naki na kanki?
Kwarai kuwa, ko da nayi aure burina shi ne in zama daya daga cikin manyan fitattun masu shirya fina-finan Kannywood. Dan duk sana’ar da zan yi wallahi bai fi mun fim ba Kuma ba na son barin shi domin fim na iya da kyau a rayuwana.
Wace shawara za ki bai wa ‘yan mata masu shiga harkan fim a yanzu?
E, toh. Shawarata ga kannena ‘yan fim masu tasowa ita ce, musamman ma mata sai kun bi a hankali Kuma ku yi amfani da lokacinku ku yi abubuwa masu amfani don lokaci a cikin harkan nan da ya wuce shikenan fa. Don haka nake jawo hankalinku da ku yi amfani da lokaci ku yi ma kanku tsari mai amfani don kar ku cinye lokacinku a banza, ya zamana an yi da na sani daga baya. Kuma Ina rokon Allah da ya kare ku daga sharrin zamani, Allah ya ba mu mazajen nagari amin.
Wane sako gareki ga masoyanki
Sakona ga masoyana shi ne godiya ta musamman domin da bazarku nake rawa har yanzu, kuma ku sani cewa ina nan cikin kwanciyar hankali, daga karshe ina muku fatan alheri a duk inda kuke ni ma ina son ku har raina, na gode
Mun gode sosai da hadin kan da kika ba mu
Ni ma na gode, Allah ya kara daukaka amin. Na gode.