Daga Sabo Ahmad
Hukumar daidaita hasken wutar lantarki ta ƙasa, ta bayyana cewa, duk wanda aka kama da laifin satar wuta, zai biya tarar naira 450,000.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana cewa, daga yanzu za ci tarar duk wanda ke amfani da wuta ba tare da mita ba, tarar wadda a yanzu ta kai naira 450,000 maimakon naira N50,000, da ake yanke wa a baya. Hukumar ce ta fitar da wannan doka ce bisa amincewar wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 da ke faɗin ƙasar nan.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta amince da wannan doka, wadda ministan wuta da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya sa wa hannu.
Yayin da Mataimakin shugaban Hukumar, Sanusi Garba, ke magana a kan, batun samar da mitar ya ce, ya faro ne lokacin da kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Jos, ya gaya wa minista Fashola da sauran mahalarta taron da aka saba gudanarwa wata-wata, inda aka amince da cewa, dole a samar da hanyar da za a tabbatar ana cajin masu amfani da wuta gwargwadon wutar da suka yi amfani da ita.Wakilinmu na musamman da ke ma’aikatar wuta da da ayyuka da gidaje ne ya ruwaito mana wannan labarin wanda ya ci gaba da cewa, a cikin sashin rahoton da Garba ya bayar ya ce, “ Abin da ya rage a wannan doka shi ne, kawai ta fara aiki, sai dai duk da haka, wajen yanke hukuncin za a yi la’akari da wanda ya saci wutar lantarkin” inji shi.
Haka kuma rahoton ya nuna cewa, Fashola ya shawarci Hukumar da ta wayarwa da abokan hulɗarta kai, yadda za su fahimci babban rikicin da ke tattare da satar wutar lantarkin, don su tsira daga faɗa wa cikin tarkon wannan doka. Sannan ya shawarci hukmar da abin ya shafa ta tabbatar ta hukunta dukkan wanda aka samu da laifi.