Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Duk Wani Kudin Fiton Kaya Asusun Gwamnati Yake Shiga –DC Muhammad Auwal

by
4 years ago
in TATTAUNAWA
4 min read
Duk Wani Kudin Fiton Kaya Asusun Gwamnati Yake Shiga –DC Muhammad Auwal
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ganin irin yadda aka samu koma bayan cinikayya a Arewacin Nijeriya, musamman a jihar Kano wadda ake wa  lakabi da cibiyar kasuwanci, da kuma raguwar shigo da kayayyaki ta filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, yasa nayi waiwaye adon tafiya da nufin kara jawo hankulan ‘yan kasuwa da kuma sauran al’umma a dangane da yadda za su rika shigo da kayayyakin su kai tsaye zuwa Kano daga kasashen duniya, a maimakon bida su ta wasu kasashe kamar irin su Kotano a Jamhuriyar Benin da Lome a kasar Togo.

Wannan tsinkaye ya biyo bayan irin korafe-korafen da al’umma keyi, bayan da gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hana shigo da Shinkafa da kuma motoci ta kan iyakokin kasa, sai dai kawai ta tashoshin jiragen ruwa da kuma sama.

Binciken da na yi ya tabbatar mana da cewa yanzu haka akwai tashoshin jiragen ruwa  akalla guda takwas da kuma na sama guda hudu a kasar nan, ciki har da na Dakta Nmandi Azikwe dake Abuja da kuma fiilin jirgin saman Mallam Aminu Kano. Dan kasuwa nada damar aiko da kayansa kaitsaye zuwa Kano ko Kaduna, kuma ya dauki kayansa ba tare da bata wani lokaci ba.

Labarai Masu Nasaba

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

A yanzu haka Jirgin kaya guda kacal daga kasar Turkiya ke jigilar kaya zuwa Kano. Ko da shi din ma  kayan da yake kawowa bai taka kara ya karya ba. Amma idan muka dubi filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Ikko, A kowanne mako akwai akalla jiragen kaya goma dake sauke kayyaki daga kasar Waje, kuma masu wadan nan kayan zaka iske sun fito daga kudancin kasar nan ne. wannan ya sa na tuna  da wata Karin Magana hausawa dake cewa, “Idan Bera nada sata daddawa ma nada wari.”da kuma Gyara kayan ka baya zamowa sauke mu raba.

A yunkurin jawo hankalin ‘yan kasuwa da su farka daga barcin da suke, ya sa na yi tattaki zuwa filin sauka da tashin Jiragen saman Mallam Aminu Kano domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin fiton kayyayaki, a inda na samu zantawa da mataimakin Kwanturola Muhammad Auwal, wato Jami’i mai kula da Na’ura mai kwakwalwa da kuma biyan kudin fito na Hukumar hana fasa kwauri ta Kwastan, shiyyar Kano da Jigawa.

Mai karatu zai so sanin takaitaccen tarihin DC Muhammad Auwal?

An haifi Muhammad Auwala Unguwar Soron Dinki dake cikin Birnin Kano, ya fara karatun firamare a makarantar Lebanon School dake Kano, sannan ya tafi makarantar sikandiren kimiyya ta garin Dawakin Kudu a jihar Kano. Bayan ya kammalla karatunsa na Sikandire sai ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria,inda ya kammala Digirin sa a farko a shekarar 1988.

Mataimakin Konturola Muhammad Auwal ya fara aiki da hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya a shekarar 1990. A yanzu haka shi ne jami’in dake kula da Na’ura mai kwakwalwa da kuma karbar kudin fito a ofishin Huhumar Kwastan shiyyar Kano da Jigawa. Kuma yanzu haka ofishin sa yana flin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

ADVERTISEMENT

Ko mene ne cikakken aikin da ka DC Muhammad ke jagoranta?

Da farko da komai da muke yi wajen  biyan kudin fito na hukumar kwastan a na’ura mai kwakwalwa (computer) akeyinsu, don hakane anan mutum zaizo idan ya shigo da kayansa daga kasar waje. Idan aka shigo da kaya daga kasar waje, kafin kaya su so akwai abin daa ake kira ‘manifest’ wato bayanin dake nuna irin kayan da aka shigo da su ko ta jirgin ruwa ko ta jirgin sama. Kafin kaya su iso, za a aiko mana da bayaninsu ta kwamfuta wato ta hanyar yana gizo, kuma za mu ajiye, sai lokacin da mai kaya ya zo ya fada mana shi ne wane, kayansa sunzo a jirgi kaza, lokaci kaza, za mu duba a cikin na’ura mai kwakwalwa mu gani. Idan kayan sunzo sai mu bude masa hanya yadda zai bi yaje banki ya biya kudin fiton daya kamata ya biya, bayan nan ne zai je a duba kayan domin tabbatar da cewa abin da ya shigo da su su ne.

Ba za ku iya duba kayan da mutum ya shigo dasu ba, kafin mutum yaje banki ya biya kudin fito. Ko sai ya je ya biya tukunna?

A bisa tsari da ake da shi yanzu na biyan kudin fito da karbar kaya, kai da kanka za ka ce ka kawo kaza, sannan ka tafi banki ka je ka biya kudin fito domin kowanne kaya daka sani akwai kudin da doka ta tsara za a biya. Idan ka biya wannan kudin a banki, ba kai zakace mana ka biya ba, su Bankin ne za su aiko mana da sako ta yanar gizo ta kwamfuta, sai bayan ka biya kudi fito a gabanka za a zo a bude kwantenar ka, ko kazo ka bude da kanka. Za mu ga cewa abin daa ka gaya mana gaskiya ne? Idan gaskiya ne za mu barka kadau kwantenarka ka tafi. Idan kuma an sami kuskure akwai hanyoyin da za a bi a gyara, ko a kara maka kudin fiton domin yai dai-dai. Idan kuma haramtattun kaya ne za a kwace a kai su wurin ajiya na gwamnati.

A kowanne irin Banki za a biya kudin fito? Kuma a asusun kwastan za a sanya kudin ko a asusun gwamnatin tarayya?

Ba kowanne banki za ka je ba, duk jami’in fito da yayi rijista da hukumar kwastan za a bashi sunayen bankunan da gwamnatin tarayya ta aminta su karbi kudin fito, kuma su wadannan Bankuna suna da alaka da yanar gizo da hukumar kwastan. Haka kuma asusun bana kwastan bane na gwamnatin tarayyane, mu hukuma ce dake karkashin gwamnatin tarayya.

Jama’a na kukan cewa, ganin yadda kuke tara kudi da yawa, sai abin da ku ke so ku ke yi da kudi, meye gaskiyar hakan?

Ba haka bane, kudin nan fa da muke karba na fito a madadin gwamnatin tarayya, ba tsagwaran kudi ake bamu ba, Banki ake zuwa a biya a asusun gwamnatin tarayya. Don haka bamu da hurumin taba wannan kudi, mudai kawai za mu gani ne a kwamfuta ance ka biya wannan kudi, kuma bisa ka’ida da ka biya kudin daya dace an ce ka zo ka dauki kayan ka.

Bisa ga yadda na gani zuwana ofishinka, mutum na iya sanya wakili ya zo ya karba masa kayansa, ko kuma ya zo ya karba da kansa, wane Karin haske za ka yi wa jama’a?

A ko da yaushe idan aka shigo da kaya kuma ba ka san dokoki da ka’idoji na daukar kaya ba, to akwai wakilai (agent) domin akwai irin wadannan wakilai da aka sahalewa damar gudanar da irin wannan aiki. Suna nan da yawa, kana iya samun sunayensu a ofishin mu mafi kusa da kai.

Za mu neme ka ne kawai idan aka samu matsala, musamman idan ka shigo da haramtattun kaya, za mu fara rike wannan wakilin naka (Agent) shi kuma ya bayyana mana inda kake, ko kuma ya kawo mana kai domin ka fuskanci hukuma.Ibrahim

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Gidauniyar MALPAI Ta Bada Tallafin  Kudin Karatu Ga Yara Mata 700 A Kebbi

Next Post

Nijeriya Na Sake Fuskantar Barazanar Tattalin Arziki

Labarai Masu Nasaba

APC Da PDP

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

by Yusuf Shuaibu
1 month ago
0

...

Buba Marwa

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

by
1 month ago
0

...

Dakta Yusuf Sani

Ba Na Jin Dadin Yadda Ake Yi Wa Malaman Jami’a Kudin Goro — Dakta Yusuf Sani

by Yusuf Sani
2 months ago
0

...

Hodar

Rikita-rikitar Badakalar Hodar Ibilis Ta Su Abba Kyari

by
3 months ago
0

...

Next Post

Nijeriya Na Sake Fuskantar Barazanar Tattalin Arziki

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: