Connect with us

MUHALLI

Dumamar Duniya

Published

on

Muna wani mawuyacin lokaci ne a tarihin duniya, lokacin da bil’adama zai zabi irin rayuwansa nan gaba. Yayin da duniya ke ci gaba da dogara ga juna a rashin karfi ko kumamanci, rayuwa nan gaba ta kunshi yanayi na masifa da alkawarai manya-manya.

Kafin dai mu kai ga ci gaba dole ne, sai mun fahimci cewa a cikin al’adu da halin rayuwa daban-daban masu kayataswa; mu al’umman iyali guda ne na duniya da makoma guda.

Kamata ya yi kuma mu hada kai wajen tabattar da jurewar al’ummar duniya, wanda ke kafe kan dabi’u na kwarai mai daraja halittu, da daraja ’yancin bil’adama a duniya.

‘Yancin tattalin arziki da kuma al’adar zaman lafiya. A dangane da haka ne, mu al’ummar duniya muka furta hakkokinmu ga juna,domin rayuwan dukan al’umman duniya da kuma tsarraraki masu zuwa.

Canjin yanayi ko dumamarsa, wani batu ne da yake ci gaba da daukar hankalin bil’adama kuma yana jawo zazzafar muhawara da musayar ra’ayi tsakanin masana da kwararraru, musamman kan illolin da wannan batun ke haifarwa a rayuwar al’umma.

Sakamakon ayyukan yau da kullum da mutane ke yi a muhallinsu na ci gaba domin rayuwa da kuma harkokin yau da gobe da masana’antunmu ke yi na kirkiro hanyoyi na samar da saukin rayuwa ga bil’adama hakan na da matukar tasiri ga rayuwa wadda ke shafar harkokin noma da kiwo sakamakon fitar da wasu sinadarai masu guba ga muhallin da muke rayuwa a cikinsa. Canjin yanayi na faruwa ta hanyoyi da yawa fiye da misali amma akwai wadanda suka fi suna da saurin gurbata muhalli kamar su yawan fitar da hayakin masana’antu, kona taya, zub da shara ba bisa ka’ida ba, amman wuta daga duwatsu da sauran su. Narkewar kankara alama ce ta dumamar yanayi.

Duk wadannan al’amura na haifar da abubuwa da dama kamar samun rauni ga tattalin arziki, rashin tsaro, hijira duk suna karuwa sosai sakamakon sakacin gwamnatocin da suka gabata har ma wadanda suke kai sakamakon zaman barkatai da aka bar mu muna yi ba tare da an sanya ido akan illolin wannan al’ada ta halin ko’in kula da muka saba ga muhallinmu,wanda na iya durkusar mana da tattalin arziki sakamakon lalacewa da kasar noma ke yi da rage mata daraja kuma hakan na jawo masifu da yawa ga gwamnati da ‘yan kasa baki daya.

Bincike ya nuna cewa yawaitar ‘yan gudun hijira da masu neman takardun izinin zama a Turai da sauran kasashe da suka ci gaba na faruwa sakamakon baci da kasar noma ta yi a yawancin kasashe masu taso wa sakamakon canjin yanayi da ke afkuwa ta dalilin rashin kulawa da me zai je ya komo , saboda haka ne ya zama wajibi ga gwamnatoci musamman wadanda suka ci gaba su samar da kudade na tallafi ga kasashe masu taso wa don gyaran muhallinsu domin suna daga cikin masu bata shi ta hanyar amfani da makamashi don kere-kere wanda kaso ma fi tsoka sukan hake su a kasashe masu taso wa.

Masana sun yi ittifaki cewa, duk yawancin tashin-tashina da ke faruwa a duniya na faruwa ne sakamakon neman kare ma’adanai ko kasar noma daga cin iyaka da makotan kasashe ke yi wa juna musamman kasashen da suka ci gaba ko wadanda ba su da yawan fadin kasar noma. Wannan na jawo asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin naira duk shekara, idan muka dauki kasashe kamar su Siriya an yi asara rayuka da dukiya da dama sakamakon fadan kabilanci wanda duk hakan na nuni da cewa canjin yanayi na da tasiri a kan abin da ke faruwa a irin wadannan kasashe.

 

Gurbata kasa noma a gurin hakar Fetur

Yawan ‘yan cirani na duniya na karuwa sosai sakamakon karyewa tattalin arziki duniya kuma hakan na nuni da cewa tabarbarewa ingancin kasar noma na da alaka da yawan fitar samari da ‘yan mata zuwa manyan birane na duniya domin samun abin sanyawa a baki, wanda hakan wani ma’auni ne babba da ke nuna tasirin da canjin yanayi ya kowa ga rayuwar bil’adama sakamakon kankancewa kasar noma da kiwo.

Gudun hijra dalilin canjin yanayi Nijeriya na fama da matsaloli kamar su Boko Haram a jihohin Barno da Yobe , fada tsakanin Fulani (Makiyaya) da Manoma A jihohin Taraba,Biniwai da Ikiti duk wannan sakamakon rashin kyawawan tsari  daga bangaren gwamnatocinmu, domin duk gwamnatin da ba ta hasashen me zai faru a lokaci mai tsawo tana tare da afkawa cikin wannan halin da muka tsinci kanmu a yanzu wanda abin Allah ya kyauta idan ba a samu an yi tsari na kirki ba to na tabbata abin da zai faru gaba sai ya nunka haka, domin rashin tanadi da hangen nesa ba zai kai mu ga ko’ina ba sai halaka da tabewa.

Sakamakon ci gaba da aka samu ta bangaren lafiya yawan jama’a na duniya ya habaka wanda hakan kuma na zama barazana ga dan abin da ya yi saura da muka samu na asali a duniya da kuma hadama ta bil’adama ya jawo tabarbarewa duniya ta hanyar karin zafi a cikin duniyarmu wanda hakan na janyo tabarbarewa lafiya da tattalin arziki da walwala, hakan kuma na iya zama barazana ga yara, mata da tsofaffi ta fuska tsaro da walwalarsu. A kwanakin baya ne duniya ta sha mamaki sakamakon gano samari maza da mata a kasar Libiya da aka mayar da su bayi da aka yi a wannan kasar wanda yawancinsu ‘yan Afirka ne, kuma da yawansu kasashensu na fama da yake yake da fari da karyewa tattalin arziki wanda hakan ne ya jawo masu ficewa domin dole zuwa kasashen da ke da arziki domin samun abin rayuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: