Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Duniya Ta Yi Maraba Da Sabuwar Shekarar 2021

by Idris Aliyu Daudawa
January 1, 2021
in RAHOTANNI
2 min read
Sabuwar Shekarar 2021
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Al’ummomi a fadin duniya sun hana idanuwansu bacci domin dakon shigowar sabuwar shekarar miladiyya ta 2021 cikin dare zuwa wayewar garin yau.

Kamar yadda aka saba, mabiya Addinin Kirista sun hallara a majami’u domin gabatar da addu’o’i da murnar shigowar sabuwar shekarar.

samndaads

Daga lokacin da ya rage saura minti daya agogo ya nuna sha biyun dare ya yi, galibin wadanda suka hallara a majami’un sun rika kirga dakikokin da suka rage lokacin ya cika wanda cikarsa ke da wuya; kowa ya barke da shewa da murna domin nuna farin ciki da shigowar sabuwar shekarar.

Masu gabatar da wa’azi daban-daban, sun yi wa jama’a nasiha a kan komawa ga Ubangiji domin ya jikan bayinsa musamman ya yaye wannan bala’i na korona da ya addabi duniya.

Bikin sabuwar shekarar dai, akan yi bukukuwa sosai domin nuna murna da shigowarta, kamar dai idan mutu ya samu sabuwar mota, sabon dinki, sabon aure, gida, aiki, kai akwai abubuwan da za ayi ta bayanai kan su a matsayin sabo ko sabuwa.

Bikin sabuwar shekara wani biki ne da jama’a suke yi wannan kuma na duniya ne gaba daya, sai dai yadda ake bikin ya sha bamban ne daga wannan gari zuwa wancan, ko kuma daga wannan kasa zuwa waccan haka ne shi al’amarin na bikin sabuwar shekara irin ta miladiyya yake kasancewa. Wasu suna barin jihohin da suke aiki zuwa jihar su inda garin nasu yake ko kuma kauye saboda yin bikin sabuwar shekara, da akwai kuma masu yin tanajin kudade na musamman domin yin cefanen zuwa gida bikin na sabuwar shekara kurum.

Wasu ma’aikatan da kuma masu yin wasu al’amuran tafiyar da rayuwa ta yau da kullun daban- daban su kan tafi zuwa wuraren su ne, ko kuma su ma’aikatan su dauki hutu wanda zai hade da kai su zuwa sabuwar shekara, a gida domin su ga ‘yan’uwansu da abokan arziki. Saboda kuwa wasu sai irin wannan lokacin ne su ke samun damar ta ganin ‘yan’uwansu da abokan arziki wadanda suka rabu da gani na wani lokaci.

Akwai abubuwan da mutane kan shirya na musamman saboda shi bikin na sabuwar shekara, bama kamar tanaje- tanajen abubuwan da za ayi na ciye- ciye, lashe- lashe da kuma tande- tande a ranar, duk ana tanadar su ne, musamman ma da yake shekara ce ta miladiyya da zarar an ce ma karfe goma sha biyun dare ya yi, to daga wannan lokacin ne fa za a fara yin shagali sai gari ya waye, a kuma ci gaba gaba dayan wannan ranar haka masu bikin za su yi tayi. Ga kuma kade- kade, wake- wake da kuma bushe- bushe da kuma raye- raye duk saboda murnar shiga  ita sabuwar shekarar.

Dai- dai lokacin da wasu suka fara harkokin su na bukukuwan sabuwar shekarar ta miladiyya ne da ake fara shi da karfe homa sha biyun daren, haka nan ma akwai wadanda suke zuwa wuraren ibadu su roki Allah madaukakin Sarki ya hada su da alkhairan suke wannan sabuwar shekarar, wadanda kuma suke ba na alkhairi ba ya raba su da su. Kamar yadda shi al’amarin Allah yake kasancewa sau da yawa ko mafi akasari wani ko wasu a cikin sabuwar shekarar ce Allah zai masu wani budi na samun wani abu a ranar ma, ko kafin ita shekarar da kare.

SendShareTweetShare
Previous Post

KAROTA Ta Cafke Inyamurin Da Ya Yi Safarar Tabar Wiwi Katon 60 A Kano

Next Post

Zaki Da Dacin 2020 A Nijeriya

RelatedPosts

Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

Sam Nda-Isaiah Ya Rasu Lokacin Da Ake Tsananin Bukatar Gudunmawarsa – Jami’ar Jos

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Shugabannin jami’ar Jos sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da...

Kasuwar Mile 12

Kwamitin Da Shugaban Kasuwar Mile 12 Ya Nada Na Cigaba Da Jajanta Wa Manoman Arewacin Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Sabon kwamitin da Babban Shugaban kasuwar mile 12 Intanashinal market...

Sojoji Sun Farmaki Mahakar Ma’adanai A Zamfara, Sun Cafke ‘Yan Bindiga 150

Ranar Mazan Jiya: Babu Wani Abin Murna Ga Tabarabrewar Tsaro – Dattawa Ga Buhari

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Dattawan Nijeriya a karkashin inuwar gamayyar kungiyar wato (COPANE), sun...

Next Post
2020 A Nijeriya

Zaki Da Dacin 2020 A Nijeriya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version