CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Duniya Za Ta Amfana Da Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Kasar Sin

by CRI Hausa
November 25, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Sin Na Fatan Raba Gajiyar Binciken Da Take Yi A Duniyar Wata Da Sauran Sassa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ranar Talata 24 ga watan Nuwanban shekarar 2020 ne, kasar Sin ta yi nasarar harba na’urar bincike ta Chang’e-5, a wani aiki da ya kasance mafi sarkakiya cikin jerin ayyukan binciken duniyar wata da kasar ta aiwatar, binciken da ya kara bude wani sabon babi a harkar binciken sararin samniya.
Duk da cewa, ita ce kasa ta uku, bayan Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet da suka gudanar da bincike a duniyar wata, kasar Sin ta sha alwashin raba samfuran da na’urar za ta dawo da su doron duniyarmu tare da sauran sassa gami da masu binciken sararin samaniya
Idan har wannan aiki ya yi nasara, zai kasance irinsa na farko da ya kunshi dauko samfura daga duniyar wata, tun bayan da Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet suka gudanar a shekarun 1960 da 1970.
Duba da muhimmancin hakan ta fuskar binciken kimiyya. Masana na cewa, binciken sararin samaniya aiki ne da ke shafar rayuwar daukacin bil Adama, duk da haka kasar Sin na fatan bunkasa shi ta hanyar musaya, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Abin da ke kara bayyana kiraye-kirayen kasar Sin na yin hadin gwiwa da samun nasara tare.
Bugu da kari, wannan mataki na kasar Sin, ya kara nuna muhimmancin cudanyar bangarori da kasar ke fatan ganin ya kankama. Hannu daya, in ji masu iya magana, ba ya daukar Jinka.
Kasar Sin ta sake bayyana kudirinta na yin aiki tare da sauran kasashe, don ba da gagarumar gudummawa kan yadda za a gudanar da ayyukan bincike da yadda zai amfani bil-Adama cikin lumana, da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama
Shin ko sauran kasashe, za su yi koyi da kasar Sin wajen gudanar da ayyukan bincike da cin gajiyar sararin samaniya cikin lumana ga daukacin bil-Adama? Rana aka ce ba ta karya, sai dai Uwar Diya ta ji Kunya. Kasar Sin dai ba za ta sauya manufarta ta samun ci gaba cikin lumana ba. (Ibrahim Yaya)

SendShareTweetShare
Previous Post

Sin Da Afirka Na Hada Kansu Domin Yaki Da Cutar COVID-19

Next Post

Dan Kwallo Diego Maradona Ya Kwanta Dama

RelatedPosts

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

by CRI Hausa
13 hours ago
0

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wasu mutane sun...

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

by CRI Hausa
13 hours ago
0

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya saurari...

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

by CRI Hausa
13 hours ago
0

A kauyen Huikeng a garin Xinwan na gundumar Xiushui a...

Next Post
Likitan Maradona

Dan Kwallo Diego Maradona Ya Kwanta Dama

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version