Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka

byCMG Hausa
3 years ago
Duniya

Ran 3 ga watan nan, babban bankin Amurka ya sake sanar da kara kudin ruwa da kashi 0.75%, da nufin sassauta hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida. Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku illar da wannan mataki zai haifar.

Wannan shi ne karo na 6 da babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa tun farkon bana, matakin da ya sa kudin ruwan ya kai matsayin koli tun watan Jarairu na shekarar 2008.

  • Tsegunta Barazanar Tsaro Daga Ofishin Jakadancin Amurka: Wa Abin Zai Amfanar?

Sai dai ba a kai ga daidaita matsalar hauhawar farashin kaya ba, a maimakon haka, matakin ya kara haifar da koma bayan tattalin arzikin duniya.

Bankin duniya ya ba da rahoto cewa, yawancin manyan bankunan kasa da kasa sun kara kudin ruwa a kasashensu da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 50 da suka gabata sakamakon matakin da Amurka ta dauka. Abin da ya haifar da mummunan tasiri ga kasashe masu tasowa wadanda ke matukar bukatar ci gaba.

Kwanan baya, an saurari ra’ayin masana tattalin arziki 100 a duniya, inda suke ganin cewa, kudin ruwan da Amurka ta kara a jere, ya haifar da koman baya a duniya baki daya, kuma 90% na masanan da aka tattauna da su, sun yi hasashen cewa, saboda da mataki na Amurka, ana fuskantar karin kalubalen hauhawar farashi.

Amurka ta samar da karin kudaden dala da nufin sassauta matsalar da ta fuskanta da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a cikin gida, amma hakan bai kai ta ga samun nasara ba.

A maimakon haka ma, sai matakin ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kara gibi tsakanin mawadata da talakawa. Ba yadda zai yi sai babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa, idan ba haka ba, jama’a za su nuna adawa da gwamnati, da haddasa rashin tabbas a zamantakewar al’umma, kana rikici da koma baya a cikin gida zai tsananta matuka.

Amma, matakin da Amurka ke dauka ya shafi wasu kasashe marasa karfi, wadanda farfadowar tattalin arzikinsu ke da rauni, baya ga haddasa hasara da mummunan sakamakon da zai biyo ga irin wadannan kasashe.

‘Yan siyasar Amurka ba su yi la’akari da muradun jama’a da rikicin da sauran kasashe za su fuskanta ba, abin da ya dame su shi ne moriyar siyasa da ta sanya gaba. Kuma suna sane da cewa, duniya za ta dandana kudar matakan da suka dauka, kamar wannan karo da ta kara kudin ruwa. (Mai zane da rubuta:MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Wata Tsaleliyar Budurwa A Indiya Ta Angonce Da Kare    

Wata Tsaleliyar Budurwa A Indiya Ta Angonce Da Kare    

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version