Kocin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ronald Koeman, ya ce ba shakkah kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yi musu wanka da ruwan sanyin da ke bayyana gaskiyar halin da suke ciki na matsalolin da suka tilasta musu fuskantar kalubale.
Koeman ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan lallasa su da PSG ta yi da ci 4-1 a haduwarsu ta farko a zagayen gasar Zakarun Turai na biyu da aka fafata a filin wasa na Nou Camp dake birnin Barcelona a kasar Spaniya.
Koeman ya bayyana cewa duk da cewa an zura musu kwallaye hudu a raga amma duk da haka ba su fitar da ran cewa za su samu nasara ba a kan kungiyar ta PSG idan an buga wasa na biyu a kasar Faransa.
“Duk da haka ina da kwarin gwiwar cewa zamu samu nasara a kansu a fafatawa ta gaba da zamuyi dasu saboda kwallo ce komai zai iya faruwa idan munje kasar Faransa buga wasa na biyu kuma ina fatan zamu samu nasara” in ji Koeman
Yayin wasan na ranar Talata dai matashin dan wasan PSG Kylian Mbappe ya nuna kansa inda ya ci kwallaye uku, ya yin da shima dan wasa Moise Kean ya ci kwallo daya, a bangaren Barcelona kuwa Messi ne ya ci mata kwallon guda daga bugun fanareti.
Sai dai kaftin din Barcelona Lionel Messi yana shan caccaka daga wasu magoya bayan kungiyar, da kuma masu sharhi kan kwallon kafa, dangane da gazawar da wasu ke ganin yayi wajen taimakawa Barcelona ya yin wasan da PSG ta lallasa su da 4-1 har gida Camp Nou a gasar Zakarun Turai.
Tsohon dan wasan Chelsea Joe Cole ne na baya bayan nan da ya caccaki Messi, wanda ya ce alamu sun nuna cewa zuciyar kaftin din ba ta tare da kungiyar sa saboda gaba daya bai buga abinda akayi zaton zai buga ba.
Joe Cole ya kuma gargadi kociyan Manchester City Pep Guardiola da cewar, ya guji kulla yarjejeniya da Messi domin a cewarsa a halin yanzu kallon kitse ake yiwa rogo domin ba irin Messin da aka sani bane a shekarun baya.
A kakar wasan da ta gabata dangantaka tayi tsami tsakanin Messi da Barcelona, bayan da suka sha mummunan kayi a wasan gasar Zakarun Turan da Bayern Munich ta lallasa su da ci 8-2 a zagayen kusa dana kusa dana karshe.
A waccan lokacin dai Messi yayi yunkurin tilastawa Barcelona kyale shi ya sauya sheka kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyar sa da kungiyar, wadda a karkashinta yake da zabin rabuwa da ita a karshen kakar wasa, ko da kuwa wa’adin yarjejeniyar bai kare ba.
A halin yanzu kungiyoyin da ake alakanta Messi da su sun hada da kungiyar kwallon kafa ta PSG wadda ake ganin zaije ya hadu da tsohon abokinsa Neymar da kuma Manchester City wadda zai hadu da tsohon mai koyar dashi wato Pep Guardiola wadda kuma a shekarar bara suka soma tuntubar juna.