Dybala Yana Son Komawa Madrid

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dan kasar Argentina, Paolo Dybala ya nuna sha’warasa ta komawa Real Madrid a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar tafara fita daga ransa kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Dybala wanda yakoma Jubentus daga kungiyar kwallon kafa ta Palermo a shekara ta 2015 ya zura kwallaye 68 cikin wasanni 142 daya bugawa kungiyar sannan kuma ya a duk shekarun dayayi a kungiyar sai da ya lashe kofin siriya A.
Kakar wasan data gabata dai itace kakar wasan datafi kowacce a gurin dan wasan baya daya zura kwallaye 26 cikin wasanni 46 daya buga kuma kwallaye 22 daya zura duk a gasar siriya A ya ci.
Sai dai har yanzu dan wasan bai zura kwallo a raga ba tun bayan komawar Ronaldo kungiyar wanda hakan yasa ake ganin dan wasan zaiso yabar kungiyar saboda yana ganin soyayayar da magoya bayan kungiyar suke masa tafi ta Ronaldo yanzu.
Kungiyar Real Madrid dai har yanzu bata maye gurbin Ronaldo ba wanda hakan yasa ake ganin kungiyar zata kai tayin kudi a kakar wasa mai zuwa domin ganin ta siyi dan wasan idan har abubuwa basu canja a kungiyar ta Jubentus ba.
Ronaldo da Dybala dai har yanzu basu zura kwallo a raga ba a gasar siriya A bayan buga wasanni uku da Jubentus yayinda Real Madrid itama duk ta lashe wasanninta guda uku na farkon laliga kamar yadda Jubentus din itama ta lashe a gasar siriya A.

Exit mobile version