Abubakar Abba" />

ECOWAS Ta Bada Tallafi Ga Kungiyar Samar Da Takin Zamani A Afirka

ECOWAS

Kungiyar ECOWAS ta taimaka wa Kungiyar samar da takin zamani a nahiyar Afirka (WAFA) a taron gidauniyar tara dala miliyan 520 da sashen zuba jari da samar da ci gaba banki (EBID) na kungiyar ta ECOWAS ya dora wa kasashen ‘ya’yanta su bayar.

WAFA ta bai wa EBID damar tara jimlar dala miliyan 430 na kudaden da aka shigo da takin zamani da kuma dala miliyan 90 na jarin da aka zuba.

A cikin wata sanarwa da ECOWAS ta fitar ta hanyar sashenta na noma, kula da muhalli da kuma albarkatun ruwa, ya wayar da kan kasashen ‘ya’yanta taretare da kuma kara masu kwarin gwiwa domin su kara Saudi wajen fara shirin gabatar da takardun da za su fara gudanar da ayyuka da ba da ban da za su bukaci kudade.

Bugu da kari, Hukumar ta kara da cewa, shirin ya kuma kunshi yawan takin zamani da aka shigo da shi tare da kuma irin kafawar da masu ruwa da tsaki a da suka mallaki masana’antun sarrafa takin zamani a kasashen ‘ya’yanta.

Har ila yau, manufar taimakon shi ne, domin a kara samar da da takin zamanin, wanda har yanzu, a nahiyar ya your karanci, har ila yau, hukumar ta kuma ja hankalin ministoci na ma’aikatun aikin noma cewa, duk da kokarin da aka yi wajen noma Shinkafa ‘yar cikin kasa, har yanzu wacce aka noma ba ta wuce kashi 60 a cikin dari ba na iya bukatar da ake da ita a cikin kasar, musamman idan aka yi la’akari da wacce aka kiyasta an yi amfani da ita a shekarar 2019 ta kai tan miliyan 24, inda hakan ya nuna cewa, yankin ya yi asarar dimbin kudaden musaya na kasar waje ta hanyar yawan shigo da Shinkafa daga kasar waje.

Hukumar ta yi nuni da cewa, idan aka yi la’akari da shirin na kungiyar WAFA da kuma dabarun da ECOWAS ta samar, musamman a fanin noman Shinkafa, a shirye take wajen ganin an habaka fannin na aikin noma a nahiyar ta hanyar samar da wadataccen takin zamani.

A wata sabuwa kuwa, a bisa yunkurinta na habaka kiwon Kifi, musamman irin na Tilapia, Gwamnatin jihar Anambra ta yi alkawarin gina wuraren kiwon Kifi daidai da na duniya ako wacce uku da ke a fadin jihar, musaman don samar da ayyukan yi ga yan jihar.

Furuncin hakan ya fito ne daga bakin Babban Manajin Darakta na hukumar ciyar da kasuwancin dabbobin ruwa (AFABDA) Mista Emeka Iloghalu.

Babban Manajin Darakta na hukumar bunkasa kasuwancin dabbobin ruwa, Mista Emeka Iloghalu ya sanar da hakan ne a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a yankin Awka.

A cewar Babban Manajin Darakta na hukumar ta kasuwancin dabbobin ruwa Mista Emeka Iloghalu, don gwamnatin Gwamnan jihar Willie Obiano ta samu cin nasarar wannan kudurin na ta, Gwamna Willie Obiano, tuni ya dauko kwararru a fannin daga hukumomi da ban-da-da ban don su fara duba wararen da ya da ce a gudanar da aikin sanan kuma su gabatar ma sa rahoton bincikensu.

Babban Manajin Darakta na hukumar ciyar da kasuwancin dabbobin ruwa Mista Emeka Iloghalu ya ci gaba da cewa, wuraren da ake son yin, kwarrun tuni sun duba halin da su ke ciki a yanzu, inda ya kara da cewa, an fara duba wuraren.

Babban Manajin Darakta na hukumar ciyar da kasuwancin dabbobin ruwa Mista Emeka Iloghalu ya bayyana cewa, hukumar ta AFABDA tuni ta na kan ci gaba da tattaunawa da hukumar zuba jari da bayar da kariya ta jihar ta Anambra (AIPPA) don ta taimaka a samar da kasuwa yadda mutanen da zasu amfana a karkashin shirin, za su samu bunkasa a fannin.

A cewar Babban Manajin Darakta na hukumar ciyar da kasuwancin dabbobin ruwa Mista Emeka Iloghalu, an fara yin kokarin aikin ne ta hanyar yin hadaka da Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Anambra da kuma kamfanin Dula da ke kasar nan, inda ya kara da cewa, kamfanin kwararre ne a fannin kuma zai yi dukkan iya kokarin sa wajen cin nasarar aikin.

Exit mobile version