ECOWAS Ta Dakatar Da Mali Saboda Juyin Mulki Sau Biyu

Daga Sulaiman Ibrahim

Sakamakon Juyin mulkin da sojojin kasar Mali suka yi sau 2 cikin watanni 9, Kungiyar ECOWAS ta sanar da dakatar da Kasar Mali daga cikin kasashe mambobinta.

Sun bayyana hakan ne a taron da shugabannin kasashen kungiyar suka gudanar jiya a Ghana.

Kasar Ta Mali ta kasance cikin kazamin rashin tsaro, Sakamakon kai hare-hare da kungiyoyin ikirarin jihadi ke yi.

Taron wanda ya gudana jiya Lahadi bisa jagorancin shugabannin kasashe 10 da ministocin waje 2 a birnin Accra na Ghana ya mayar da hankali kan halin da Kasar Mali ke ciki.

Ministan harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor ya ce dakatarwar da aka yiwa Mali daga jerin kasashen ECOWAS zai fara aiki ne nan ta ke daga jiya Lahadi 30 ga watan Mayu har zuwa watan Fabarairun 2022 lokacin da aka tsara Sojin za su mika mulki ga zababben shugaban farar hula.

Taron na ECOWAS wanda ya samu halartar masu shiga tsakani a rikicin siyasar Malin, karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya karkare da bukatar ganin lallai kasar ta tabbatar da nadin farar hula a matsayin jagoran gwamnati.

Sanarwar da ECOWAS ta fitar bayan taron, ta bayyana cewa shugaban gwamnatin sojin da mataimakinsa da firamininstan na Mali basu da damar tsayawa takarar zaben da aka shirya gudanarwa a kasar don mika Mulki ga fararen hula kuma don tabbatar da dimukradiyya.

Exit mobile version