ECOWAS: Yarjejeniyar Yaki Da Laifukan Fashi, Safarar Mutane A Teku

Masananin tsaron ruwa Abubakar Abdulsalam, ya ce, irin wannan yarjejeniyar aiki tare, ba shakka za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron yankin.

Rundunonin sojojin ruwan Kasashen Yammacin Afirka sun kulla wata yarjejeniyar aiki tare, don kawo karshen sata da safarar gurbataccen mai, da ma sauran miyagun laifuka a ruwan yankunan.

Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojin ruwan Nijeriya, Bice Admiral Ibok Ekwe Ibas, ya ce, wannan yarjejeniyar ta kunshi aiki tare tsakanin dakarun ruwan yankunan Kasashen Yammacin Afrika, domin kawo karshen matsalar sata da safarar gurbataccen mai a Kasashen.

Admiral Ibok, ya kara da cewa, suna sane da irin kazarkazar din miyagun a hankoronsu na tafka danyen aikin, amma ya yi gargadin cewa su ma fa sojojin ruwan a shirye suke wajen tunkarar duk wani takadari da yake son bijirewa, duba da yanzu gungun rundunonin kasashen ne za su dinga daukar matakin bai daya.

Babban Hafsan mayakan ruwan Nijeriyar ya kuma nanata shirinsu na tabbatar da shawo kan matsalolin fashin teku, safarar mutane da ma sauran laifukan da miyagu ke tafkawa ta cikin ruwa.

Masananin tsaron ruwa Abubakar Abdulsalam, ya ce, irin wannan yarjejeniyar aiki tare, ba shakka za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron, musamman duba da yadda a ruwan yankin akwai inda ba mallakin kowace Kasa ba ne, inda nan ECOWAS ce ke da iko da shi, don haka shigowa cikin batun da ta yi, zai saukakawa dakarun aikinsu.

Exit mobile version