Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta yi wa dan wasanta na gaba Edison Cabani tayin rika biyanshi euro miliyan daya a matsayin alawus na musamman, domin lallashinsa ya rika bai wa Neymar damar bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A makon daya gabata ne aka samu sa’insa tsakanin Neymar da Cabani, bisa wanda ya dace yayi bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka samu nasara kan Lyon da kwallye 2-0, a waccan lokacin dai duk da bukatar amfani da damar bugun da Neymar ya nuna, Cabanin ne ya buga kuma ya gaza jefa kwallon a raga.
A wani yunkurin kawo karshen takaddamar ce, shugaban kungiyar ta PSG Nasser Al-Khelaifi ya yi wa Cabani tayin rika biyanshi alawus na euro miliyan daya, sai dai Cabani yaki amincewa da hakan.
A jimlace, tun daga kakar wasa ta 2013 zuwa yanzu, Cabani ya ciwa kungiyarsa ta PSG kwallaye 95 a wasanni 140 da ya buga.