Aliyu Ahmad" />

Editan Jaridar Rariya Aliyu Ahmad Zai Angwance Yau

Tsohon ma’aikacin sashen Hausa na Kamfanin LEADERSHIP Group Ltd kuma Editan Jaridar Rariya a yanzu, Malam Aliyu Ahmad, yana angwancewa a yau Juma’a.

Bayanan da muka samu daga angon sun bayyana cewa za a daura aurensa da sahibarsa Hauwa Sa’idu Gambo, da misalin karfe 2:00 na ranar Juma’a, 12 ga Fabrairun 2021 a masallacin Juma’a na Muhammadu Buhari International Market da ke garin Karu a yankin Abuja.
Kasancewar Aliyu dan asalin kabilar Igala ne a Jihar Kogi kuma ga shi ya nemi bafulatana, an tambaye shi ko ya samu matsala wurin neman auren sat un da ana wa Fulani kallon ba sa ba da aure idan ba ga junansu ba?
Sai ya ce, “Tabbas, ni dan yaren Igala ne, amma wacce zan aura Bafulatana ce. Alhamdu lillahi, ban samu kalubale ba, addini ya wayar da mutane. Duk wannan batun kabilacin an aje shi a gefe, yanzu haka kanwata Bahaushe ta ke aure.”
Ko me dan jaridar zai ce game da wannan nasara da ya samu ta aure da Allah ya ba shi? Sai ya ce, “Alhamdu lillah, babu abin da zan ce sai godiya ga Allah.

“Wannan wani lokaci ne na farin ciki da mutanen da mu ke zaman mutunci da su su ke jira. Na ga kara da mutane ke nuna min. Ina godiya a gare su baki daya.”
Shi dai Aliyu, a yanzu shi ne ke gudanar da shafin jaridar Rariya a Facebook, wadda ta kasance daya daga cikin manyan wuraren da ake samun labarai a soshiyal midiya.

Exit mobile version