Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), ta bayyana cewa ta ƙwato Naira biliyan 365.4 a shekarar 2024 tare da samun nasara kan mutane 4,111 da aka gurfanar a kotu.
Shugaban hukumar, Ola Olukayode, ya jinjina wa ma’aikatansa kan sadaukar da kai da suka yi don cimma waɗannan nasarori.
- Tattalin Arzikin Al’Ummar Kasar Sin Na Tafiya Yadda Ya Kamata A Watan Jarairu Da Fabrairu
- Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya
Ya bayyana hakan ne a wani taron kwanaki uku da hukumar ta shirya a birnin Uyo, Jihar Akwa Ibom.
Ya ce EFCC na ƙoƙarin inganta aikinta ta hanyar aiki da gaskiya da ƙwarewa domin yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa.
A nasa jawabin, Farfesa Tonnie Iredia ya ce rashin fahimta da murɗa labarai na daga cikin matsalolin da ke hana jama’a fahimtar ainihin aikin EFCC.