Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a shiyyar Legas, sun kama mutane 32 bisa zargin su da hannu a zamba ta hanyar kwamfuta. Wadanda ake zargin sun hada da; Anthony Nicholas, Obabire Adebayo, Nwosu Ebuka, Obiora Udenta, Adeoye Dabid, Oni Oluwabunmi Olasunkanmi, Oiseomaye Mike, Ifeanyi Godwin da Obabire Tunde.
Sauran su ne: Okafor Chibueze, Damilare Moronfayo, Micheal Makanjuola, Samuel Oyindamola, Haruna Mubarak Okiki, Opeyemi Hassan, Salami Junior, Yusuf kuadri, Adediran Waris, Idoko Shedrack, Andrew Agbai, Mercy Adedoyin, Olamide Mubarak, Damilare Babalola, Idris Mutairu, Adebiye Michael, Idris Adasofunjo, Rasak Adasofunjo, Olawaye Olayemi, Amodu Idris, Adeniyi Ahmed, Shittu Usman da Oli Maduabuchi Charles.