Umar A Hunkuyi" />

EFCC Ta Cafke Wani Lauyan Karya

Hukumar yaki da cin hanci da karban rashawa (EFCC) ta kama wani mutum mai shekaru 53, mai suna, Muhammed Bolaji Abdulraheem, a bisa zargin karyar nuna kansa a matsayin Lauya.

Ana kuma zargin mutumin da karban kudade ta hanyar karya.

Abdulraheem, wanda jami’an hukumar ta EFCC suka kama shi daga sashen su da ke Ilorin, ana kuma zarginsa da damfarar wani mai suna Mallam Yusuf Bello, tsabar kudi naira dubu 300,000.

Bello, a cikin karar da sashen yakar ta’addanci na hukumar ta EFCC ya gabatar, ya yi zargin wanda ake tuhumar ya kwato wani bashin sa na naira 300,000, daga wanda yake bi bashi sannan ya yi ikirarin cewa wai kudin suna hannun hukumar ta EFCC.

Lauyan karyan an yi zargin ya yi wa kansa shaida da cewa sam bai kai wa hukumar ta EFCC kudin ba, ya kara da cewa, hukumar ta EFCC ba ta san komai ba a kan maganar.

A wani abu mai kama da was an kwaikwayo, wanda ake tuhuman jiya sai ya lalata bayanan da ya bayar a inda ya aminta da cewa lallai shi Lauya ne, yana kuma gudanar da aikin na shi na Lauya sama da shekaru 20.

A binciken da hukumar ta aiwatar ya tabbata cewa, wanda ake tuhuman bai kammala karatunsa a makarantar koyon aikin Lauya ta kasa ba, domin bai iya cin jarabawar makarantar ba har karo biyu.

Exit mobile version