EFCC ta cafke wasu mutane 11 da ake zargi da zamba ta hanyar intanet a Osogbo.
Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa, EFCC, a shiyyar Ibadan, a ranar Juma’a, 22 ga Janairu, 2021 ta kama mutum 11 da ake zargi da zambar intanet.
Jami’an hukumar sun damke su ne, ta hanyar amfani da bayanan sirri, Wanda hakan yasa aka samu nasarar gano maboyar su a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Hukumar ta kwato motoci 12 wadanda suka hada da Toyota Highlander SUVs 3, Mercedes Benz GLK 350 SUV, Acura SUV, Honda Crosstour 2, Toyota Venza 2 da kuma wasu motocin Toyota guda 3.

Haka kuma an kwato wayoyi, kwamfutocin laptop da sauransu.
Wadanda ake zargin, wasu acikinsu sunyi ikirarin ce wa su dalibai ne, wasu ‘Yan gidan wasa ne, wasu manoma ne da kuma ‘yan kasuwa, a halin yanzu ana ci gaba da yi musu tambayoyi don tabbatar da aikata laifin.
Za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.