Hukumar EFCC ta Najeriya ta ce ta kama wasu ‘yan damfara ta yanar gizo guda goma sha bakwai a garin Kaduna, su de ‘yan damfarar an yi nasarar damke sune ne lokacin da suke kokarin samun wajen mafaka a jihar Kaduna. Shugaban hukumar a shiyyar Kaduna Malam Mailafiya Yakubu shine ya tabbatar da hakan lokacin da yake yi Wa manema labarai karin bayani.
Ya ce “Hukumar na shawo kan kalubalen da ke kawo cikas a gaban kotunan wannan kasa, jami’an mu ta fannoni daban-daban sun fito suna farautar su a wajen da suke zuwa domin hutawa, to mu kuma muna wajen muna wajen muna jiransu. Ranar da muka fara zuwa mun yi nasarar damke guda takwas, rana ta biyu muka kama bakwai.
“Wannan basyan mun koma muka kara kama guda biyu, wanda ya zauna lafiya shi ya so yanzu muka fara, kuma nan bada jimawa ba zamu gurfanar da su a gaban kotu domin a yanke musu hukuncin da ya dace da su. Kuma muna da hujjoji da muka samu iya gwargwado.
“Sannan akwai kwararan hunjoji a hannun mu da muka tanada wajen gurfanar da su a gaban kotu, dan kuwa ko kwanakin baya a Abuja, mun samu nasarar kama mutane guda dari hudu, bayan mun kai su kotu an yanke musu hukuncin da yayi daidai da su.
“Kuna cin nasarar sosai amma zaka gani cewa an barwa hukumar EFCC kadai ace sune zasu ji da komai, amma ya kamata ya zama abinda mutum ya gani ya kamata ya taimaka maka. Sai yace bazai yi ba ya bar maka kayan kane, wanda mu kanmu jami’an muna samun barazana sosai.
“Wani lokaci sai mutum ya kira ka a waya yana cewa kaine kake wannan bincike,to kayi gaggawar bari Idan ba haka ba to zaka ga abinda zai same ka. Wasu daga cikin mu suna rasa rayukan su ta wannan hanya, mu kuma mun lashi takwabin cewa za muyi wannan aiki baji ba gani babu tsoro.
“Saboda mun san cewa amma shi Allah yasan aikine mai kyau, kuma da shi mu ka dogara shi ne zai kare mu a duk inda muke.”
Batun yaki da cin hanci da rashawa de yana cikin manya-manyan alkawuran da mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi, sai de wadandan su ‘yan kasa na ganin cewa kawo wadannan ayyyukan badakarlar, aiki ne tukuru gaban gwamnatin saboda yadda cin hanci da rashawa ya shiga jini da jiki na al’ummar wannan kasa.