EFCC Ta Kama Gwaggo Matar Ganduje

Daga Sulaiman Ibrahim,

Hukumar EFCC ta damke Hafsat Ganduje, uwargidan gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan zargin cin hanci da rashawa.

Kamun ya zo makonni bayan gazawar uwar gidan kan kin amsa gayyatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa tayi mata.

Tun da farko an gayyaci Hajiya Hafsa Ganduje ta kai rahoto hedikwatar EFCC a Abuja a ranar 13 ga Satumba, kamar yadda aka ruwaito a baya, amma ba ta bayyana a gaban hukumar ba.

Majiyoyin da ke kusa da ita daga baya sun ce ta yi tafiya zuwa Burtaniya don halartar bikin kammala karatun ɗanta a lokacin da aka nemi ta bayyana agaban hukumar.

EFCC tana tuhumar Hafsa Ganduje kan zarge -zargen da suka shafi zamba cikin filaye a cikin karar da danta, Abdualzeez Ganduje ya shigar.

Wani mutum, wanda ke da masaniyar kamun amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce “an kama ta da yammacin jiya (Litinin).”

Exit mobile version