EFCC Ta Kama Mutane Shida Bisa Almundahana A Ibadan

A ranar Litinin ne, a ka kama mutum shida wadanda a ke zargin su da aikata laifukan da su ka shafi almundahana da dukiyar jama’a a Ibadan babban birnin Jihar Oyo, lokacin da jami’an hukumar cin hanci da rashawa, wato EFCC su ka kai farmaki a mabuyarsu da ke rukunin gidajen Kolapo Ishola Estate a yankin Akobo cikin jihar.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, an kai wannan farmakin ne bisa irin korafe-karafe da mutanen unguwar su ka kai wa hukumar, inda su ka bayyana mata irin laifukan da su ke aikatawa. Su wadanda a ke zargi da aikata laifin ba su wuce shekaru 24 zuwa 30, an dai bayyana sunayensu kamar haka Tella Adefemi Ibrahim, Awoniyi Adeseye Abiodun, Oladele Olawale Wasiu, Olabiti Afeez Ajibola, Akeredolu Oluwafemi Temidayo da kuma Oyaremi Olalekan Olabode.

Majiyar tamu ta kara bayyana cewar, bayanan asirin da a ka samu ne ya sa a ka yi tunanin cewa, lalle ruwa baya tsami banza, dole ne su kasance suna aikata irin laifukan wadanda su ka hada da dukkanin ayyukan cuta ta internet. An dai samu kayayyaki masu yawa da ga wurinsu, kamar manyan motocin hawa masu tsada guda biyar, kwamfuta, wayoyi da kuma wasu abubuwan da su ke amfani da su wajen cutar mutane, wadanda kuma tuni sun yi magana dangane da hakan.

Exit mobile version