Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) shiyyar Kaduna sun cafke mutane 40 da ake zargi da yin damfara ta intanet a garuruwan Bida da Minna a jihar Neja.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da layu, Ɗankamfai na mata, motoci uku, komfuta Uku, janareta da kuma na’urar sanyaya iska.
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N835 Kan Kowace Lita
- Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi
An kama waɗanda ke zargin ne a wani samame da aka yi a jere a garuruwan jihar Neja, tun daga ranar Talata.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale ya tabbatar da kama mutanen