Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta sake gano wasu manyan gidajen Alfarma mallakar Tsohuwar Ministar Mai, Diezani Alison- Maduekwe a Daular Tarayya Larabawa wato, Dubai.
A cewar rahoton, an gano gidajen Biyu ne a Dubai sakamakon binciken da wasu jami’an kasar ta yi, cewa kadarorin mallakar dan Nijeriya ne.
Wata majiya ta ce, an kiyasta kudaden gidajen guda biyu a kan Naira Bilyan 7.1.