Bello Hamza" />

EFCC Ta Yi Babban Kamu A Tashar Jirgin Sama Na Abuja

Hukumar EFCC, ta cafke gwal da darajarsa ya kai fiye da Dala 3,131,412.39 dai dai da Naira 1,127,308, 460.39 da ake kokarin fita dasu zuwa garin Dubai, ta kasar United Arab Emirates, ba a kan ka’ida ba.

Bayanai sun nuna cewa, hukumar EFCC sun ambaci sunan wani Abba Ali Yahaya a matsayin wanda yake jagoran badakalar.

Bayan karbe takardar tafiyar Mista Abba, an kuma kwace fiye da Fam 112,000 wanda bai gabatarb wa hukuma ba, wannan ya kuma saba wa dokar badakalar kudade na kasa ‘Money Laundering (Prohibition) Act.’

Ma’adanan masu dan karen tsada da aka kama a hannu Abba ana da tabbacin cewa, wasu masu hakan ma’adanai ba tare da izini ba da suke hakan ma’adanai a jihar zamfara ne suka ba shi ya fitar musu da shi.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, a halin yanzu mutum 4 daga cikin ‘yan kungiyar na fuskantar shari’a, bayani ya kuma nuna cewa, sun kware wajen fita da kayayaki ba tare da jami’an tsaro dake aiki a fikin jiragen sama na kasar nan sun ankara ba.

Kamar dai yadda wata takarda da wakilinmu ya gani take bayani, wannan da ake zargin ya bayyana cewa shi dan aike ne kawai, gungun jami’a tsaro ne karkashin jagorancin wata mace ne suka cafke shi a filin saka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe.

Bayanin ya kuma nuna cewa, wanda ake zargin ya tsallake dukkan matakan tsaro da na’urorin dake a filin jigin saman, amma daga baya aka kama shi.

Wani ne ya tsegunta wa jami’an tsaron halin da wanda ake zargin yake a ciki bayan ya tsallake kusaan dukkan matakan bincike na tsaro a filin jirgin saman.

“yana tare da gwala gwalai day a kai na naira biliyan 1.1 don ta hadu da abokan tafiyarsa a can Dubai wadanda suka shahara wajen sayen gwala gwalai da aka hake sub a tare da izini ba. kasancewa tare da gwal ba tare da izini ba karya dokan hakan ma’adamai na kasa ne.

“An kuma kama Abba da fam 112, 000 wanda bai gabatar wsa da jami’an kwastam ba an kuma kama shi da katin fitar da kudi har guda 19. Bayan an bincike sa ne ya bayyana cewa, shi dai dan aike ne kawai, ya kuma nuna wani dan kasuwa a mastayi wanda ya tura shi, sai dai daga baya an gano cewa, karya ne ya na kokarin kala wa mutumin ne kawai.

“Tuni hukumar EFCC ta shi ga farautar mutanen da ke hakan ma’adanai ba tare da izini ba a jihar Zamfara don hujjojin da ake da shi a hakin yanzu ya nuna cewa, suna tare da  wannan mutumin da aka kama.

“Mun kwace takardar tafiyarsa mun kuma kwace gwalawala, gwalagwalan a aka kwace sun kai na Fam 112,000 ya mannasu ne a cikin jikinsa, kuma dokar yaki da cin hanci da rashawa ya mallaka wa gwamnatin tarayya wadanna dukiyar gaba daya.

“Hukuamr EFCC za ta mika bukatar tag a babban kotun tarayya don neman a ,mallaka mata wadanna kudaden da aka kama a hannusa, doka tab a shi izinnin tafiya da dala 10,000 a duk zirga zirgansa.

“A halin uanzu an bayar da belin Abba, ana kuma ci gaba da binciken yadda lamarin ya kasance.”

Ya zuwa rubuta wannan labarin, ana bincikar yadda wanda ake zargin ya wuce ta gaba na’urorin ba tare da sun bankado shi ba.

Majiyar gwamnati ta kuma kara da cewa, “abin takaici ne a ce ga mu da na’u’rori daban daban na bincike wadanda jami’an tsaro daga bangarori daban suke gudanarwa amma sun kasa gano wanda ake zargin.

“Lallai muna zargin hadin baki da wasu jami’an tare da wanda ake zargin, don kuwa babi mamakin wadanna ‘yan ta’adda sun samu sun malaki wasu daga cikin jami’an tsaronmu a filayen jiragen sama na kasar nan.

“Binciken da zamu gudanar zai muna mana yadda ya tsallake matakan jami’an tsaron dake aiki a filin jirgin saman gaba daya.”

 

Exit mobile version