Rabiu Ali Indabawa" />

EFCC Ta Yi Dirar Mikiya A INEC

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi dirar mikiya a babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na INEC reshen jihar Sakkwato a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba.

Rahoton ya bayyana cewa, jami’an na EFCC sun yi awon gaba da wasu manyan jami’an hukumar INEC domin su amsa muhimman tambayoyin da EFCC ta shirya musu.

Majiyar ta ruwaito wasu jami’an ofishin INEC da ke jihar Sakkwato sun tabbatar da kamen, sai dai ba su yi karin bayani game da yanayin laifin da a ke tuhumar da jami’an da a ka yi awon gaba da su ba, sakamakon ba su da izinin yin magana da ‘yan jaridu.

Idan za a tuna a ‘yan kwanakin bayan nan ne hukumar EFCC reshen jihar Sokoto ta kama wasu jami’an INEC guda hudu a kan laifin karkatar da wasu kudi Naira miliyan 84.6 hakkokin ma’aikatan da su ka gudanar da zaben 2019 da su ka ki biyan su.

Kaakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa EFCC ta kama mutanen ne sakamakon kara da wani Abdullahi Nasiru ya shigar gabanta a madadin kafatanin ma’aikatan zaben wucin gadi da suka gudanar da zaben 2019 a jihar Zamfara.

Sai dai wasu ma’aikatan wucingadin sun tabbatar da cewa sun fara samun kudadensu da sanyin safiyar Talata 29 ga watan Oktoba ta asusun ajiyan kudadensu na banki.

Exit mobile version