EIC: Masu Zuba Jari Na Kasar Sin Na Karfafa Ci Gaban Tattalin Arzikin Habasha
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EIC: Masu Zuba Jari Na Kasar Sin Na Karfafa Ci Gaban Tattalin Arzikin Habasha

byCGTN Hausa and Sulaiman
12 months ago
EIC

Hukumar zuba jari ta kasar Habasha ko EIC ta ce, masu zuba jari na kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen karfafa ci gaban tattalin arzikin kasar Habasha, ta hanyar zuba jari mai dimbin yawa, da samar da ayyukan yi. 

A cikin wata sanarwar da hukumar ta EIC ta fitar da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata, ta bayyana cewa, a cikin shekarun da suka gabata wasu ayyuka 3,309 na kamfanonin Sin, sun zuba jari fiye da dalar Amurka biliyan 8.5 a kasar Habasha, lamarin da ya ba da gudummawa sosai ga manufofin tattalin arzikin kasar.

  • Yunƙurin Kafa Ƙasar Yarbawa: Igboho Ya Miƙa Koke Ga Firaministan Birtaniya
  • An Kama Wani Matashi A Jigawa Saboda Ƙona Kakarsa

EIC ta kuma bayyana cewa, karuwar masu zuba jari na kasar Sin, ta fuskar yawan ayyuka da kuma kudaden dake shigowa, ta samar da kuzarin da ake bukata a tattalin arzikin Habasha.

Wadannan jarin sun samar da sama da 325,400 na guraben ayyukan yi na dindindin da na wucin gadi ga Habashawa a cikin ‘yan shekarun nan, a cewar EIC. Bayan wata babbar ziyara da tawagar EIC ta kai yankin masana’antu na Gabas mai nisan kilomita 40 a kudu maso gabashin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, hukumar ta bayyana cewa, sama da kamfanoni 150 ne ke aiki a yankin, inda masu zuba jari na kasar Sin suka kai sama da kashi 95 cikin dari na wadannan kamfanoni.

Yankin masana’antu na Gabas, wanda masu zuba jari masu zaman kansu na kasar Sin suka gina, ana daukarsa a matsayin abin koyi ga raya yankin masana’antu na kasar Habasha, wanda hakan ya kara karfafa burin Habasha na zama cibiyar masana’antu na Afirka. (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Haɗama, Son Kai Da Jahilci Ne Sanadin Wahala A Nijeriya – Obasanjo

Haɗama, Son Kai Da Jahilci Ne Sanadin Wahala A Nijeriya - Obasanjo

LABARAI MASU NASABA

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version