Abubakar Abba" />

El-Rufai Bai Goyon Bayan Maida Mulki Kudu A 2023 – Kungiyar Nasiriyya

Magoya  bayan Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed  El-Rufai a karkashin kungiyar  Nasiriyya ta kasa ta karyata rahotanin da wasu kafafen yada labarai na shoshiyal midiya su ka wallawa na cewa Nasiru el-Rufai ya na goyon bayan mayar da shugabancin Nijeriya zuwa Kudu ‎a shekarar kakar babban zaben 2023.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin  sanarwa da Shugaban kungiyar ta Nasiriyya ta kasa Dakta Modibbo Yakubun Farakwai da Sakatare Janar dinta na kasa Dogara Ibrahim Aliyu su ka sanyawa hannu su ka kuma baiwa LEADESHIP A YAU a Kaduna.
Kungiyar ta bayyana rahoton na shoshiyal media a matsayin labaran kanzin kure wanda kuma baida wani tushe balle makama.
A cewar kungiyar, Malam Nasir Ahmed el-rufai ako da yaushe yana goyon bayan chanchanta ne da kuma iya kwarewa na shugabanci, amma ba goyon bayan shugabanci na karba-karba a kasar nan.
Shugaban kungiyar ta Nasiriyya ta kasa Dakta  Modibbo Yakubun Farakwai da kuma Sakatare Janar dinsa  Dogara Ibrahim Aliyu, sunyi nuni da cewa, ko wanne haifaffen dan Nijeriya yana da yancin tsayawa takarar kujerar shugabancin Nijeriya ko daga wani yaki shi ko ita ya fito.
Kungiyar ta Nasiriya ta kara da cewa, ko kusa Gwamna  Nasir el-Rufai bai furta mayar da shugabancin Nijeiya ba a zuwa kudancin kasar nan ba a shekarar 2023 ba.
Kungiyar ta kuma yi kira gay an Nijeriya dasu yi watsi da rahoton na shoshiyal media dumin babu abinda ke cikin sa sai tsagwaron karya.
Shugaban kungiyar ta Nasiriyya ta kasa Dakta  Modibbo Yakubun Farakwai da kuma Sakatare Janar dinsa  Dogara Ibrahim Aliyu, sun sanar da cewa baza su gajiya ba wajen bayar da goyon baya don a samar da shugabanci mai darewa a kasar nan da zaman lafiya  da kuma ci gabana kasar nan.
A karshe, kungiyar ta kuma yi kira ga daukacin alummar jihar Kaduna kada su gajiya wajen irin dimbin goyon bayan da suke baiwa gwamnan jihar Malam Nasir Ahmed  El-Rufai, musamman yadda yake kan kokarin wanzar da romon dimokiradiyya ga daukacin ’yan jihar ba tare da nuna wani bambanci ba.

Exit mobile version