Rahotanni sun kawo cewa ‘yan majalisar dokokin Jihar Kaduna sun shiga alhini da rudani sakamakon sanarwar da Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi a ranar Asabar, na cewar sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar Coronabirus.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, sanarwar da El-Rufai ya yi ya sanya fargaba a zukatan wasu ‘yan majalisa musamman wadanda suka yi aiki dab da dab da shi a makon da ya gabata, domin basu san ya yi gwajin ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu mambobin majalisar ma sun shiga killace kansu tun bayar sanarwar, yayin da Shugaban ma’aikatan Gwamnan, Mohammed Sani Dattijo wanda kan kasance tare dashi a koda yaushe ya yi gwaji kuma sakamako gwajin ya nuna cewa baya dauke da cutar.
A wata sanarwa da Uwargidan Gwamnan Jihar kaduna, Hajiya Hadiza El-Rufai, ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta bayyana cewa za a kai samfarin jininta gwaji a ranar Lahadi sannan ta yi godiya ga ‘yan Najeriya kan addu’o’insu da fatan alkhairi da suka yiwa Mijin na ta, wato Gwamnan Malam Nasir El-rufai.
Akwai rahotannin dake bayyana cewa, tuni suma Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Dakta Hadiza Balarabe da Sakataren Gwamnatin jihar, Malam Balarabe Lawal Abbas, suma sun yi nasu gwajin.
Sai dai wakilinmu ya tattaro cewa tun bayan sanarwar wasu kwamishinoni da hadiman gwamanan sun shiga damuwa, a inda daya daga cikin kwamishinan ya bayyana cewa koda dai bai hadu da gwamnan ba na tsawon makonni biyu da suka gabata, amma ya hadu da manyan jami’an gwamnati wadanda suka hadu da gwamnan.r
Wakilinmu ya ruwaito cewa koda dai gwamnan bai yi tafiya zuwa wajen kasar ba a wata guda da ya gabata, kuma bai halarci taron gwamnonin APC da shugaban kasa Buhari ba a ranar 16 ga watan Maris, amma ya kasance a taron majalisar tattalin arziki a Abuja a ranar 19 ya watan Maris inda ya hadu da wasu daga cikin takwarorinsa Gwamnoni ciki har da Bala Mohammed na Jihar Bauchi wanda shi ma ya tabbatar ya na dauke da da cutar ta korona barus.