El-Rufa’i Ka Kawo Mana Dauki, Har Yanzu Ba Mu San Matsayin Gidajenmu 380 Ba – Mazauna Tsaunin Kura            

El-rufa'i

Daga Abubakar Abba Kaduna

Mazauna yankin Tsaunin Kura da ke gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi cikin Jihar Kaduna da aka rusa masu gidaje akalla 380, sun koka tare da bukatar Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed el-Rufai ya agaza ya kawo musu dauki domin su san matsayin matsugunansu.

A zantawar da suka yi da LEADERSHIP Hausa, sun bayyana cewa da kudadensu suka sayi filayen kuma suka gina, wanda ba mallakar gwamnatin Jihar Kaduna ba ne, inda suka ce asalin wurin gonakin jama’a ne suka sayar musu.

Da yake yi wa wakilinmu jawabi a madadin sauran wadanda rusau din ya shafa, Malam Ibrahim Haruna ya ce, mun shafe sama da shekaru goma muna zaune a yankin tun kafin Gwamnatin Jihar Kaduna ta zo da maganar gina babban titi a yankin.

Ya ci gaba da cewa, “Ba za mu iya yin jayayya ko fito -fito na fito da gwamnati ba, amma muna rokon Gwamna el-Rufai ya taimaka ya bar mana matsugunanmu, haka kuma muna son mu san matsayin matsugunan namu daga gun gwamnatin jihar, domin ba mu da inda ya wuce mana matsugunan musamman ganin cewa akasarinmu talakawa ne kuma idan wannan damar ta kubuce mana, za mu shiga cikin halin kakani-ka-yi tare da iyalanmu.

“Gani ba mu da wani wuri da za mu iya komawa da zama, hakan ta tilasta wa akasarinmu dawo da kwana a cikin kwangayenmu da aka rusa, inda kuma wasun mu suka shiga gari don kama haya.”

Ibrahim ya kara da cewa, “Ba ma zargin kowa kan rusau din da aka yi mana, amma muna rokon Gwamna el-Rufai ya taimaka mana don mu dawo mu gyara matsugunanmu da aka rusa.”

Shi ma a hirasa da wakilinmu, wani dadadden mazaunin yakin mai suna Malam Awwal Usman ya ce, “Mun ga wasu sun zo suna manna mana takardun rusau a gidajenmu, inda aka ba mu wa’adin mako daya da mu fice daga cikin gidajenmu, wannan ne ya sa muka tambayesu, inda suka ce mana gwamnati ce ta turo su kuma mu kwantar da hankulanmu wai za a daidaita.

“Ganin haka ya sa muka kafa kwamti, inda ‘yan kwamitin suka same su sai suka shaida musu cewa wadannan takardun da aka manna a gidajenmu, an yi ne bisa kuskure ba nan yankin aka turo su ba, saboda haka mu kwantar da hankulanmu.”

Usman ya ce, bayan da wa’adin mako daya ya cika, sai suka ga Gireda ta zo ta fara rusa musu gidaje. Ya ce akwai wani makwabcisa da a lokacin matarsa ke kan nakuda, amma Giredar ta bi ta kan gidansa kuma matar na cikin gidan, inda nan take matar ta rasa ranta. Ya ce da hannunsu suka zabi wannan gwamnatin amma kuma ta saka masu da wannan.

Ita ma wata mata mai kimanin shekaru 60 da rusau ta shafi gidanta, Malama Aisha Umar ta shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, “Muna zaune a gidajenmu sai muka ga Gireda ta zo ta fara rusa mana gidajenmu ba mu san abin da muka yi ba.

“Mu mazauna Tsaunin Kura matanmu da mazanmu, mu muka zabi el-Rufai har da mata masu juna biyu da kuma marasa lafiyarmu, amma bai kamata ya saka mana da rusau ba.

“Ga shi sakamon canjin da muka zabar wa kanmu ya sa mun wulakanta, za mu kaskace indan el-Rufai ya kore mu daga matsugunanmu, domin ba mu san inda za mu je da ‘ya’yanmu da kuma marayunmu ba, a yanzu haka duk da an rusa mana matsugunanmu kuma ba mu da wani wuri da za mu je, dole ta sa muka dawo kwangayen muka ci gaba da zama.

Wani yanki da aka yi rusau din a Tsaunin Kura da ke Rigasa Kaduna.

Exit mobile version