Ibrahim Ibrahim">

El-rufai Ka Kori Masu Yi Maka Kafar Angulu Cikin Gwamnatinka -Kungiyar BSF

An yi kira ga Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, da yayi gaggauwar korar duk wasu masu yi masa kafar angulu a cikin gwamnatinsa.

Bayanin hakan ya fito ne daga hadakar Kungiyar masu goyon bayan manufofin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a turance ake kira da Buhari Solidarity Forum (BSF), a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar wacce ta sami sa hannun Shugaban kungiyar Ahmed Ibrahim Kajuru, kuma aka raba ma manema labarai a kaduna.

A cewar kungiyar, abin kunya ne abin takaici, ace wasu daga cikin gidan gwamnatin Jihar kaduna, kuma wadanda ake kyautata zaton na hannun damar gwamnan ne, amma sune da kansu suke yi ma gwamnan kafar angulu, domin kawo masa cikas a duk wasu harkokin ci gaba da yakeson kawo ma Al’ummar Jihar kaduna.

Advertisements

Kungiyar ta ci gaba da bayyana cewa, idan za’a iya tuna wa, a cikin makon daya gaba ne, a lokacin da gwamnan ke yi ma Al’ummar Jihar kaduna bayani ta kafar watsala labarai, gwamnan ya fito fili karara ya bayyana ma duniya cewa, akwai wasu na hannun damarsa dake aiki da shi a cikin gidan gwamnati, wadanda yake zargi sune ke yi ma gwamnatinsa kafar angulu, kuma yana sane da abin da suke aikatawa.

A bisa wannan dalili ne, kungiyar BSF take kira da kakkausar murya ga Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed elrufai, da cewa, lokaci yayi da zai zakulo irin wadannan mutane domin korar su daga Gidan Gwamnatin Jihar kaduna, tun kamin akai lokacin da zasu ja masa bakin jini su hadashi fada da kowa.

Kungiyar ta kuma yi Allah waddai da abin da ya faru a majalisar dokokin jihar kaduna, musamman inda wasu gurbatattu marasa son zaman lafiya da kishin Jihar kaduna, ke yawo a kafafen sadarwa domin naiman suna da fadanci wajen iyayen gidansu, suna bata sunan Aminin gwamnan, wato Sanata mai wakiltar Al’ummar kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa, Sanata Dakta Malam Uba Sani, da cewa wai shi ne ummul aba’isin hura wutar rikicin da ya kunno kai a majalisar dokokin jihar kaduna. A cewar su, wannan abin ayi Allah waddai ne ga masu irin wannan batanci.

Kungiyar ta kuma fito fili karara ta bayyana ma duniya cewa, babu wani ko wasu tsirarrun mutane da suka isa su shiga tsakanin Malam Nasiru El-rufai da amininsa Malam Uba Sani, wadanda aminan juna ne tun kamin zuwansu gwamnati. Kuma a cewarsu, a dalilin amintakarsu sun kawo ma jihar kaduna gagarumin ci gaba, wanda tarihi ba zai manta da hakan ba.

Daga karshe, kungiyar ta BSF tayi kira ga daukacin Al’ummar Jihar kaduna, da su ci gaba da baiwa gwamna El-rufai goyon baya akan ayyukan alheri da ya dauko domin yi ma jama’ar Jihar kaduna. A cewarsu.

Exit mobile version