Connect with us

SIYASA

El-Rufai Shugaba Ne Mai Adalci – APC Unguwar Sarki

Published

on

An bayyana Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, a matsayin gwarzo kuma adalin shugaba na gari da har abada Al’ummar Jihar kaduna ba zasu taba mantawa da irin salon jagorancinsa ba.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugabannin jam’iyyar APC reshen mazabar Unguwar Sarki a Jihar kaduna, a yayin da su ke zantawa da manema labarai, domin kara bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnan, da kuma karyata jita-jitan da wasu ke yadawa na cewa, wai tun da gwamnan ya hau mulkin jihar, har zuwa wannan lokacin babu wani abin kirki da gwamnan ya tsinana wa ‘ya’yan jam’iyyar APC reshen mazabar da gwamnan ya fito, wato unguwar sarki.

‘Ya’yan jam’iyyar ta APC reshen mazabar Unguwar Sarkin, sun bayyana cewa, duk wani abin arziki da akeso Da, dan halak ya yima Iyayensa a jam’iyyance, to, su ko shakka babu Gwamna Nasiru El-rufai ya yi masu komai, kuma har gobe su na tare da shi dari bisa dari.

Shugabannin na jam’iyyar APC sun kuma kara da bayyana cewa, “idan ana maganar samar da aiki yi ga Matasa, tuni Gwamna El-rufa’i  ya riga ya fitar da mu kunya, domin a zuwa yanzu, gwamnan ya samarwa Matasan Unguwar sarki aikin yi Maza da Mata fiye da 200, wanda suka hada da aikin KASTELEA,  daukar aikin koyarwa, aikin likita, aikin kula da muhalli, da dai sauran wasu dimbin ayyuka.”

A cewarsu, “a matsayinmu na ‘ya’yan jam’iyyar APC na mazabar unguwar sarki, wanda itace mazabar da mai girma gwamna ya fito, munaso mu kara jaddada goyon bayanmu ga irin salon mulkin jam’iyyar APC tun daga matakin kasa har zuwa na kananan hukumomi.”

“Sannan mu na mika sakon godiyarmu da fatan alheri ga irin dimbin ayyukan cigaba da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Nasiru El-rufai, Sanata mai wakiltar al’ummar kaduna ta tsakiya, Malam Uba Sani, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kaduna ta Arewa, Honarabul Sama’ila Sulaiman, Shugaban karamar hukumar kaduna ta Arewa, Honarabul Saleh Shu’aibu, Dan Majalisar mu ta jiha, Honarabul Yusuf Salihu, da kuma Kansilar unguwar sarki, duka suka kawo mana na cigaban al’ummar mu baki daya.”

Taron dai ya sami halartar daukacin Shugabannin jam’iyyar APC reshen mazabar unguwar sarki, a kalla su sama da 30, wanda suka hada da, Shugaban Jam’iyyar APC reshen mazabar unguwar Sarki, Alhaji Bala Sarkin Gida, da Sakataren jam’iyyar Abdullahi Sambo, da Ma’ajin jam’iyyar, Yahaya Usman Tela, da Sakataren tsare-tsare, Muhammed Ismail, da Aisha Muhammad, sai kuma Magajiya Ya’u, da Abdullahi Shu’aibu. Da dai sauran ‘ya’yan jam’iyyar ta APC.

Advertisement

labarai