El-Rufai Ya Cancanci Yabo Bisa Kebe Matafiya A Kaduna – Injiniya Tukur

Exif_JPEG_420

An bayyana samar da waje na musamman da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El- Rufai ya yi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna abin a yaba ma sa ne na wannan matakin da ya dauka.

Tsohon dan takarar majalisar tarayya a shiyya ta daya a karkashin jam’iyyar CPC, Injiniya Tukur Tambaya ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da wakilinmu da ke Zariya.
Injiniya Tukur Tambaya ya ci gaba da cewar, wannan mataki da gwamnan ya dauka, ya nuna shi ya damu da al’ummar da Allah ya ba shi amana ne, wato al’ummar jihar Kaduna, na kare su daga kamuwa da wannan cuta ta Korona, wanda, a cewar Injiniya, ko da matafiyi ya dauko cutar daga wata jiha, in har zai shiga jihar Kaduna, kebe shi ya na da muhimmanci kwarai da gaske.
Ya kara da cewar, yadda Malam Nasir El-Rufa’I ya mayar da wajen horas da ‘yan yi wa kasa hidima a matsayin wajen kebe matafiyar ya nuna matukar tausayi ma, a cewarsa, kamata ma ya yi mai girma gwamnan jihar Kaduna ya samar da waje na musamman a cikin daji, wato nesa da gari, a matsayin inda za a kebe matafiyan, sai ya  tsara wannan waje da aka
ambata.
Injiniya Tambaya ya nunar da cewar, ya dace al’umma su fahimci wannan cuta ta Korona, cut ace da ta addabi duniya a yau, wanda in ba a dauki matakai ma su tsauri ba, komi zai iya faruwa na matafiya daga wasu jihohi ko kuma daga wasu kasashe su shiga jihar  Kaduna da wannan cuta, ba tare da sani ba, su yada tag a al’ummar jihar ta hanyoyin da masana kiwon lafiya suka bayyana.
A game da cece-kucen da al’umma ke yi kan samar da wannan wajen kebe matafiya da gwamnatin jihar Kaduna ta yi kuwa, Injiniya Tukur Tambaya ya shawarci al’umma da ke furta batutuwan da ba su dace ba, da su fahimci batun lafiya, bai kama da siyasa ba bai kuma kama da wani abu da gwamnati za ta yi wasa da shi ba, a cewarsa, ya san gwamnan jihar Kaduna a matsayinsa na ba bangaren kiwon lafiya ya karanta ba, babu wani abu da zai yanke, sai fa ya tuntubi masana kiwon lafiya, daga nan ne zai yanke hukumcin ko wace matsala da ta shafi wannan bangare, sai ya ce, ma su fadin son zuciyarsu ya dace su kama bakinsu, shi ya fi.
Domin kare al’umma daga kamuwa da wannan cuta ta Korona kuwa, Injinya Tukur  ya shawarci gwamnonin tarayyar Nijeriya, da su tattauna da masana kiwon lafiya da suke jihohinsu, na matakan da suka dace su dauka, domin kare al’ummominsu daga kamuwa da wannan cuta ke zama tamkar wutar daji ga rayukan al’umma a sassan duniya ba arewa ko kuma Nijeriya kawai ba.
Game da kukan da al’ummar jihar Kaduna ke yin a samar da takaitattun lokuta na yin ibada a ranakun Juma’a da kuma Lahadi, Injiniya Tukur Tambaya ya yi tsokaci, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta duba yiwuwar sauraron al’umma kan batun ibada da suka bukata, sai dai kuma a cewarsa, ya dace gwamnatin jihar Kaduna ta tuntubi masana kiwon lafiya, kamar yadda ta ke yi tun daga lokacin da wannan cuta ta bayyana a sassan duniya, kafin ta yanke hukuncin kiraye-kirayen da ake yi ma ta.

Exit mobile version