El-Rufa’i Ya Musanta Hannun Khalifa Sanusi A Garambawul Da Ya Yi

Khalifa Sanusi

Daga Ibrahim Ibrahim Kaduna, 

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed el-Rufai ya karyata rade-radin da ake cewa tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sayen da ya yi a majalisar zartarwar jihar.

Idan dai ba a manta, Gwamna el-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa a ranar 12 ga watan Oktobar da ta gabata, a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Gwamnan ya nada sabbin mukamai ga wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar da yin wasu manya-manyan sauye-sauye a majalisar zartawar jihar.

Mista Adekeye ya ce, an yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da aiki mai kyau da ci gaban Gwamnati Jihar Kaduna baki daya.

Sai dai wasu da dama sun bayyana cewa tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sunusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sauyen da aka yi, inda suka ba da misali da kalaman da ya yi a wani taro bayan da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Mohammed Sani Dattijo, ya kira shi da tsohon Sarkin Kano.

Da yake mayar da martani bayan mintuna kadan a taron da aka yi a Kaduna a watan Oktoba, Sanusi Lamido Sunusi, bai ji dadin maganar ba, inda ya ce “Lokacin da na ji shugaban ma’aikatan ya kira ni da suna tsohon sarki, inda  ni ma na kira shi da tsohon shugaban ma’aikata.

Kwanaki kadan bayan afkuwar hakan, sai Gwamna Nasiru el-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa, inda ya tura Muhammad Sani Dattijo zuwa ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare a matsayin kwamishina.

Bayan sukar da aka yi ta yi kan tsohon Sarkin Kano a kan cewa, el-Rufai ya sauya matsayin tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin, Sanusi ya fitar da wata sanarwa cewa kalaman da ya yi kan maganar Muhammad Sani Dattijo a matsayin wasa ne. Ya ce ba shi da masaniya ko hannu a sauyin da el-Rufai ya yi a majalisar kwamishinoninsa.

Exit mobile version