Abubakar Abba" />

El- Rufai Ya Shelanta Cewa, Bai Da Burin Fitowa Takarar Shugabancin Kasa  A 2023

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai Gwamnan Jihar Kaduna, ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugabancin kasa a zaben kakar  2023 ba.

Gwamnan na Jihar Kaduna wanda ya sanar da hakan a  hirrasa da kafar yada labarai BBC Hausa ya ce yana son a bawa yankin kudancin Nijeriya damar su fitar da shugaban kasa a  kakakr zabe ta shekarar 2023.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai  ya ci gaba da cewa, mutane da dama sun dade suna cewa ina son yin takarar shugaban kasa tun lokacin da na ke ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Gwamna Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai  ya yi nuni da cewa, baiga wata hikima a hakan ba, inda ya ci gaba da cewa,  bana shaawar yin takarar shugabancin  kasar nan a kakar zaben 2023.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai  Allah ne ke bada mulki, ko kana so ko ba ka so kuma  idan Allah yana so, zai baka mulki, amma ni ban taba saka wa a rai ne cewa zan yi takarar shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai taba cewa na fada hakan.

Gwamnan na Jihar Kaduna ya kuma bayyana cewa, akwai yarjejeniya cewa idan arewa ta yi mulki na shekaru takwas, za a bawa kudancin kasar mulkin kuma yan siyasa sun san da batun duk da cewa ba ya cikin kundin tsarin mulki.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai  ya ce, hakan n yasa na fito na ce kada wani dan arewa ya fito neman takarar shugaban kasa bayan waadin Shugaba Buhari ta kare.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai  ya kara da cewa, duk da yana son a bawa kudancin Njjeriya damar tsayar da shugaban kasa, El Rufai ya ce a duba cancanta.

A karshe, Mallam Nasiru Ahmad a kullum cancanta ya ke duba wa ba bangaranci ba wurin nada mukamai.

 

Exit mobile version