Shugaban ‘yan uwa Musulmai da aka fi saninsu da (Shi’a) Shaikh Ibraheem El-Zakzaky, a karo na biyu ya sake kai tallafi wa ‘yan gudun hijira da ke zaune a karamar hukumar Faskari ta cikin jihar Katsina a makon da ta gabata.
Malam Rabiu Abdullahi Funtuwa shi ne ya wakilci El-Zakzaky yayin mika tallafin, ya shaida cewar, “Wannan sako ne daga shugabanmu Shaikh Ibraheem Zakzaky, da ya bayar domin a kawo muku wannan tallafin da suka kunshi kayayyakin sanyi, Barguna guda 300, gidajen Sauro guda 300 da kuma magunguna daban-daban domin jinyar rashin lafiya idan bukatar hakan ta taso.”
“Shugaban namu ya saba irin wannan aikin, idan za ku tuna a karin farko ya kawo muku tallafin abinci, amma yanzu bisa nazarin yanayin sanyi ya sanya kawo muku kayayyakin da za su fi taimakonku a irin wannan lokacin na sanyi da ake ciki sakamakon rabaku da gidajenku ba don ku na so ba; wannan tallafin ya zo ne bisa damuwa da halin da kuke shi da shi Malamin namu yi,” inji shi.
El-Zakzaky ya bayyana matsalolin tsaron da har suke haifar da ‘yan gudun hijira tabbas gazawar gwamnatoci ne wanda hakan na samu asali daga zalumcin da ake yi wa al’umma.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Malama Bilkisu Garba ta bayyana godiyarta ga Malamin a bisa tallafin da ya ba su, tana mai cewa damuwa da halin da suke ciki ma kawai da ya yi abun yabo ne, ta masa fatan kaifi.
Tunin kuma aka rabar da barguna da magunan ga wadanda aka bada tallafin dominsu kai tsaye inda suka nuna matukar farin cikinsu a bisa wannan tallafin da suka samu.