Connect with us

RAHOTANNI

EloKuence Writers Ta Yi Bikin Cikar Shekara Daya Da Kafuwa

Published

on

A ranar Talatar da ta gabata ne 22,ga Mayu, 2018, Kungiyar maruta ta EloKuence Writers Association ta yi bikin cikar shekara Daya da kafuwarta. Inda Masoya da dama suka rinKa firfito wa a shafukan sada zumunta na Facebook da Whtsapp da sauran shafuka,  domin nuna nasu farin cikin. Sauran Kungoyin marubuta online suma sun bayyana nasu farin cikin game da abin da ya samu wannan Kungiya, ciki kuwa harda EDclusiBe Writers Association daUniKue Writers Association da Real Hausa Fulani Writers Forum, da sauran su. A Bangaren Groups da ake da su na shafukan sada zumuntar suma ba a bar su a baya ba, sun firfito domin nuna nasu farin cikin game da wannan Kungiya wanda suka haDar da HaDaDDun Masoya Group da Hasken Alkhairi Group da EloKuence Writers Fans Group daTime Writers Group da Aunty Haliloss Fans Group da Smasher and Hubbiey NoBels Group da Kyautata Rayuwa Group da Er India NoBels Group  da dai sauran su. Jama’a da dama wanda ba za su iya lisafuwa ba sun firfito tare da tura saKonnin su domin taya wannan Kungiya murna, ciki har da Aunty Haliloss wadda ta yi musu Littafi shafi guda mai suna RANAR MURNA daga farkonsa har Karshensa don taya Kuniyar murna.

 

Tarihin Kafuwar Kungiyar EloKuence Writers Association

EloKuence Writers Association, Kungiya ce ta Marubutan online, wanda aka kafa ta a ranar Talata 25, ga Mayu, 2017. An kafa Kungiyar EloKuence Writers Association ne saboda hazikan Marubuta maza da mata masu fikira don su zo su ba da gudummawarsu ta basira wajen isar da muhimman saKwanni ga iyaye da samari, da ‘yan mata na zamaninmu. In da ko wani Marubuci zai KirKiro labarinsa mai Kunshe da darussa na rayuwa ko faDakarwa da ma nishaDantarwa a sauKaKe cikin salo da dabarun rubutu ta yadda saKo zai isa in da ake so ya isa ba tare da labari ya gundiri mai karatu ba yayin da yake karatu.

Wadda ta kafa Kungiyar EloKuence Writers Association ita ce, Haima Usman Zakariyya, wadda aka fi sanin ta da suna Haima Maman Abul. An kuma fara kafa wannan Kugiya ce da mutum uku Halima Usman da Shamsiyya Salis da Musa M.Sa’eed (Mr Melody Autan EloKuence). Daya daga cikin wadda aka kafa wannan Kungiya da ita Shamsiyya Salis ta bayyana cewa “Halima ita ta koyan rubutu har lokacin da ta fahimci na iya ta ce mu fara tare, ba ta da abokiyar shawara sama da ni duk wata damuwarta ba wanda take gayawa sai ni a haka muke littafi tare mu biyu da sunan ta kaDai, wanda ni na ce ta bar sunanta. A haka tai sha’awar shiga wata Kungiya suka tsaya yi mata wulaKanci a ranar ranta ya Baci ta gaya min na ba ta haKuri ta ce za ta buDe ta ta Kungiyar na ce toh ai mu biyu ne ta ce za mu samu masu shiga.

Bayan mun zo buDewa wayarta ta samu matsala sai Talented suka buDe suka kuma gayyace ni, a ranar da suka buDe na shiga, sosai na fara jin daDin Kungiyar, amma ba na sa sunan Kungiyar a littafin saboda ni da Haima muke yi na ce sai na fara tawa ni kaDai.  Da Haima ta dawo ta buDe wata ni ta fara sa wa sai Auta Mr melody, asalin sunan wani suna ne daban ba EloKuence ba, daga baya ne muka maida shi EloKuence, Cikin ikon Allah akai link akai ta shiga amma kan dare ana shiga ana fita na ce kin gani ko kawai mu koma Talented gaba Daya ta ce toh ta rufe Kungiyar washegari da safe ta ce gwamma mu jajirce da kanmu har ta Daukaka, na ce toh nai sallama da Talented saboda Haima ita ce silar fara noBel Dina ba zan taBa yi mata butulci ba na dawo muka zauna tare”. Kungiyar ta samu karBuwa a wajen Marubuta tun daga kafuwar ta har wa yau, in da tashin farko suka samu membobi mutum ashirin da biyar, sai daga bisani kuma suka rage yawan membobi goma daga cikinsu, sakamakon matsaloli da barazanar da suke fuskanta daga wajen waDan da suka tsige Din, sai suka rage su goma sha shida.

Kamar yadda Kungiyar EloKuence Writers ta samu karBuwa a wajen Marubuta, haka ma ta samu karBuwa a wajen Makaranta fiye da yadda ‘ya’yan Kungiyar suke za to. In da har Korafe-Korafe suke samu daga wajen masoyansu a kan cewar, lallai ya kamata a ce su buDe zaure in da za a rinKa samun cikakkun littafan Marubutansu cikin sauKi. Wannan dalilin ne ya sa suka buDe zauren EloKuence Writers Fans Group bayan kafuwar Kungiyar ta su da wata Daya.

Kungiyar EloKuence Writers Association tana da nagartattun jagorori nagari guda biyar masu Kwazo da aiki tukuru, waDanda suka tsaya tsayin daka don ganin cewar wannan Kungiya ta ci gaba a duniyar Marubuta littafan Hausa na online, ta kuma yi fice. Yayin da ita wadda ta kafa Kungiyar ta yi nisan kiwo ta bar amanar Kungiyar a hannunsu, ga sunayen su kamar haka:

 • Shamsiyya Salis
 • Musa M.Sa’eed (Autan EloKuence)
 • MuhieBert Abdullahi (MuhieBert India)
 • Adamu Yusuf Indabo
 • Basira Sabo Nadabo

 

WaDan nan su ne sunayen jagororin Kungiyar, nagartattu ne kuma jajirtattu masu riKo da amana da gaskiya. Baya ga haka, Kungiyar tana da membobi haziKan Marubuta masu kwazo da basira mutum goma sha Daya, ga sunayen su:

 

 • Hafsat Pure Green
 • Aysha Opera Miemie Daddy’s pet
 • Ummie Smart
 • Jannah Jay
 • Aysha Maman Bilal
 • Aisha Muhammad (Mzz Daddy)
 • Na’eerah Daughter
 • Aysha Muhammad (Kueen Nerdeey Turakee)
 • Khadija S. Dogarai (Lipton)
 • Madeenah (Hanta da Jini)
 • Hasad Abba

 

WaDan nan su ne sunayen membobin Kungiyar, Jajirtattun Marubuta ne masu Kaunar junan su, sun tsaya kai da fata sai EloKuence Writers ba gudu ba ja da baya, a ko da yaushe Kungiya ta na matuKar alfahari da su a bisa kwazon su da jajircewar su. Nasarorin da Kungiyar EloKuence Writers Association ta samu a cikin shekara Daya rak! da kafuwar ta shi ne: Kungiyar EloKuence Writers ce Kungiyar Marubutan online ta farko da a ka taBa rera wa waKa, wanda MuhieBert India ce ta Dauki nauyin waKoKin da aka rera wa Kungiyar. Nasara ta biyu da Kungiyar EloKuence Writers ta samu shi ne, ita ce Kungiyar Marubutan online ta farko da tarihin kafuwar ta ya shiga kanun labarai na Jarida. Sannan kuma Marubutan Kungiyar ne suka fara rubuta littafan Hausa Drama mai nishaDantarwa gami da faDakarwa a duniyar Marubuta Hausa na online, Marubutan littafan Draman kuwa su ne:

 

 • MuhieBert India
 • Autan EloKuence
 • Shamsiyya Salis
 • Aisha Muhammad (Mzz Daddy)

 

WaDan nan ne sunayen Marubutan littafan Hausa Draman, in da su ka rubuta a Kalla littafan Drama na Hausa guda uku, ga su kamar haka; NADAMAR DOLE, GIDAN AURE, GIDAN HAYA. WaDan nan duk nasarori ne da Kungiyar ta samu, wanda a yanzu ya zamo abin alfahari ga ko wani memba na Kungiyar, DaDin daDawa Zaman lafiya ga juna babu rikici ko kace-nace cikin wannan Kungiya sai Kaunar juna da kowanne yakewa kowa,wannan babbar Nasara ce ga wannan Kungiya, wanda ba ko ina ne ake samun hakan ba.

 
Advertisement

labarai