Connect with us

Nahiyar Afirka

Emmanuel Macron Na Fuskantar Fushi Daga Faransawa

Published

on

A Faransa, yayin da ake sa ran Shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi wa gwamnatin sa garambawul tun bayan ficewar Nicolas Hulot daga mukamin minista, wani sakamakon jin ra’ayin mutanen kasar na nuni cewa farin jinin shugaban kasar ya samu koma baya.
A wani bincinken da aka gudanar a karshen watan Agusta nan da ya shude, akala faransawa kashi 36 cikin dari suka nuna gamsuwar su da salon siyasar shugaban.
Shugaban ya samu koma baya da kusan maki shida, yayin da ministan muhalli da ya yi murabus Nicolas Hulot ya samu habaka, inda aka bayyana cewa Faransawa kusan kashi 47 cikin dari ne suka gamsu da matakin da ya dau.

Advertisement

labarai