#EndSARS: An Jikkata ’Yan Jarida Hudu Yayin Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Gombe

Shanu

A daidai lokacin da masu zanga-zangar kin jinin sashin ‘yan sanda na SARS suka fito domin gudanar da zanga-zangarsu ta mai taken #EndSARS, wasu da ba a tantance ko su waye ba dauke da adduna da su barandami sun kai farmaki inda lamarin ya kai ga jikka wakilin jaridar The Nation na jihar Mr. Shola Shittu tare da wasu uku.

Bayan shi din ma, mai dauka wa kafar yada labarai ta NTA hoto, tare da wasu ‘yan jarida duk harin ya shafa sakamakon yadda lamarin ya kazanta.

Rahotonni sun tabbatar da cewa cikin hanzari aka gaggauta kai ‘yan jaridan zuwa asibiti domin ceto rayuwarsu da samar musu da kulawar likitoci.

Masu zanga-zangar dai sun hau kan titin shataletale Yola inda suka fara jerin gwanon nasu tare da kutsawa cikin manya da kananan tituna na jihar, suna tafiya suna masu rera wakokin neman kawo karshen jami’an ‘yan sanda na SARS.

Jami’an ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin a daidai lokacin da aka fahimci wasu ‘yan daba sun kwace ragamar gudanar da zanga-zangar sabanin wanda suka faro tun da farko da suka juya da lalata kadarorin jama’a, inda nan take ‘yan sanda suka taka musu burki don gudun abun ya kazanta.

Daya daga cikin masu jerin gwanon ya shaida mana cewa, “Mun fito domin gudanar da zanga-zangarmu cikin lumana kamar yadda muka farota, amma abun takaici wasu ‘yan daba sun kotsu mana kai inda suka fara lalata kadarorin jama’a da suke kan hanya. ‘yan sanda sun zo suka tarwatsa kowa da kowa, yanzu da nake magana da kai ina hanyar komawa gidanmu,” Inji shi a daidai lokacin da ke ganawa da wakilinmu.

Jami’in watsa labarai ‘yan sandan jihar DSP Mary Mallun a lokacin da kirata, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Exit mobile version