#EndSARS: Buhari Ya Na Ganawa Da Obasanjo Da Jonathan

gwamnati

PRESIDENT BUHARI PRESIDES OVER A VIRTUAL FEC MEETING. 5. President Muhammadu Buhari, Vice President Yemi SAN and SGF Mfr Boss Mustapha during A virtual FEC Meeting held at the Council Chambers, State House, Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE. OCT 14 2020

Shugaba Kasa ganawa da wasu tsofin shugabannin Nijeriya da manyan hafsoshin tsaro. Duk da cewa ba’a bayyana ainihin dalilin ganawar ba, ana kyautata zaton taron da aka shiga misalin karfe 10 na safe kan abubuwan da ke faruwa ne a sassan Nijeriya.

Dukkan tsofaffin shugabannin Nijeriya na Soja da na mulkin dimokradiyya sun halarci taro ta yanar gizo yayinda hafsoshin tsaro da ministoci ke hallare a fadar shugaban kasa.

Daga cikin tsofaffin shugabannin kasa akwai Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar (ritaya), Goodluck Jonathan da Cif Ernest Shonekan.

Wadanda suke a fadar shugaban kasa sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; sakataren gwamnati, Boss Mustapha; Farfesa Ibrahim Gambari da Babagana Monguno.

Sauran sune shugaban hafsoshin tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Sufeto-janar na yan sanda, Mohammed Adamu; daraktan DSS, Yusuf Bichi da daraktan NIA, Ahmed Rufa’i.

Exit mobile version