A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta’azzara, musamman ta’addancin ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane, satar shanu da dabbobi da kuma rikicin makiyaya a da manoma duk a yankin Arewa; sai kuma ga wani bangare can a yankin Kudu su na neman tayar wa al’ummar kasar zaune tsaye, na tayar da jijiyar wuya a kan lallai sai gwamnati ta rushe jami’an ’yan sandan SARS, saboda a cewarsu su na cin zarafin al’umma tare da muzguna mu su ba tare da kwakkwaran dalili ba.
To, zanga-zangar tasu ta cimma ruwa, domin cikin gaggawa gwamnatin tarayya ta ji kokensu, kana ta biya mu su bukatunsu. Sai dai duk da haka ba su daina wannan zanga-zanga ba; kenan akwai wata manufa tasu boyayyiya, kodayake ba sabon abu ba ne fil a wajen ’yan kasar, domin sun dade suna yekuwa da kwaradin a raba kasar ma kowa ya san gidan ubansa, fiye da shekaru hamsin suna bisa doron manufar nan. Inda mai karatu zai tabbatar da hakan shi ne yadda wasu tsagerun yankin kudu-maso-gabas da kudu-masu-kudu suke zanga-zangar #RebolutionNow# wato zanga-zanga ce mai dauke da ma’ana guda biyu: Ko dai a yi juyin juya hali, ko kuma komai ta fanjama fanjam, a raba kasar kawai.
Yawancin masu sharhi akan al’amuran yau da kullum, sun yi amannar cewa akwai wasu jiga-jigan mutane a yankin nasu, wadanda kuma gwamnati ta yi musu riga da wando da ke daukar nauyin wadannan matasa masu zanga-zanga cikin rashin da’a da biyayya don kawo karshen mulkin duk wani dan Arewa da kuma bata masa duk wani tsare-tsarensa don ci gaban kasa, tare da nufin kirkiro da kasar Biafira.
Idan muka waiwayi tarihin baya watanni kadan bayan kisan gillar da aka yi wa shugabannin Najeriya, musamman ma ‘yan Arewa da kuma na kasar Yarbawa, hakan kuma ya kai ga kafa gwamnatin mulkin soja a karkashin Janar Johnson Thomas Amunikwe Agwuyi Ironsi, dan kabilar hafsoshin da suka hambarar da gwamnatin farar hula, ‘yan Arewa sun nemi lallai sai an yi wa wadancan azzaluman hafsoshin haddi, amma sabon shugaban kasa, Agwuyi Ironsi ya kekasa kasa ya ki, ya kuma kare su a gidan jarun don kada masu neman daukar fansa su kai gare su. Daga bisani ne kuma Janar Ironsi ya dinga fito da maitarsa a fili, har sai da ta kai ya kafa wata dokar soja mai lamba ta 32 da nufin dunkule kasar karkashin gwamnati guda don hakan ya bayar da dama ga ‘yan kabilarsa su ji dadin hawan kawara ga sauran kabilun kasar nan, suna sukwanar su yadda suka ga dama.
To amma ba a Arewar ce ba kadai aka sha tabo batun warewa daga kwaryar tarayyar Najeriya ba. A 1954 ma Cif Obafemi Awolowo ya taba tabo wannan batun sa’ilin da aka ki amincewa da shawarwari guda shida da ya kawo a wajen taron tsara sabon kundin mulkin Najeriya da zai bayar da dama a kakkafa majalisun dokoki na jihohi, yayin da ya ce idan ma haka ne to ya kamata a cikin kundin tsarin mulki a kafa wata dokar da za ta ba kowace jiha ‘yancin ficewa daga tarayyar Najeriya a dukkan lokaci da ta ga haka shi ne mafi a’ala a gare ta. Shugabannin Arewa na wancan lokacin sun yi aiki da hankali, wanda ya fi aiki da agogo, wajen nuna wa jama’ar Arewa muhimmancin ci gaba da zama a kasa daya, dunkulalliya, wacce za ta kunshi dukkan kabilun cikinta wuri guda don kowacce ta bayar da gagarumar gudummawa wajen gina kasa.
Mutanen Arewa sun kau da kai, sun hakura, sun gwammace a ci gaba da zama tare, amma saboda taurin kan wasu shugabanni, ‘yan kabilar Kudu-maso-Gabas, hakan bai yiwu ba, sai da ta kai su ga ware yankinsu da yanzu ya hada da shiyyoyin Kudu-maso-Kudu da kuma Kudu-maso-Gabas, suka kuma fice daga kwaryar Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, abin sai da ya kai ga yakin basasan da aka fafata da su na tsawon watanni talatin, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka kusan miliyan uku a dukkan bangarorin, kafin su hakura, su zauna tare da sauran jama’ar kasar nan. Amma duk da irin karimcin da aka yi masu bayan kammala basasan, da kuma irin adalcin da aka gwada masu, da taimakon da aka ba su don su tashi, su nemi na kansu, su zamanto daidai da kowa, ba su amince da yadda sauran al’ummomin kasar nan suka rungume su hannaye bibbiyu ba, ba su kuma nuna godiyarsu da irin karamcin da aka yi masu ba, sai suka ci gaba da nuna hali irin na dan magen da ke goye, wanda ke yakushin mai goye da shi.
Haka nan aka yi ta tafiya, duk gwamnatin da ta zo, walau ta soja ce ko ta farar hula sai ta nemi dadada masu, ta kuma nuna wa duniya cewa durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne. Amma su ba su san haka ba, a kodayaushe kokarinsu shi ne yadda za a daga masu kafa su ji dadin mike tasu kafar don mulkan Najeriya yadda suke so, ta yadda zai zamanto su ne za su mamaye dukkan harkoki, kuma sai yadda suka ga dama za su dama, su ba kowa ya kurba haka nan. Wadannan mutanen sun yi karfi a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda suka mayar da gwamnatinsa tamkar tasu, sai abin da suke so za ta aikata, kuma su ne suka yi kaka-gida cikin manyan jami’an da ke karkata akalarta. Sun kokarta ainun don gwamnatin Jonathan ta dore, ta yadda za su ji dadin ci gaba da tatse arzikin kasar da suka yi wa karkaf, suka bar ta ba ko karfanfana.
A wancan zamani sun bidi canja tsarin Najeriya yadda za ta dace da manufa da alkiblarsu idan sun damki ragamar mulki bayan saukar Jonathan, amma suna tasu ce Allah kuma na Nasa. Da suka ga mulki ya kubuce a hanunsu, sakamakon rashin adalcinsu da kuma zaluncinsu, sai suka dukufa wajen muzgunawa sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, suna cewa ta mayar da su shanun ware a dukkan mukaman da ta rarraba, daga bisani bayan sun fahimci inda gwamnatinsa ta dosa sai suka fara daga hakarkari, kungiyoyin farfado da Biafra MOSSOB da kuma ta IPOB suka yi ta shirya zanga-zangar da za ta iya janyo fitinar da za ta dakile manufofin sabuwar gwamnati, ko kuma su taka wa jagoranta birkin da zai kawo cikas a ayyukan alherin da yake yi wa al’umma.
Shugabanninsu da mabiyansu suka dora zazzafar tsana kan Arewa da mutanen Arewa, babu ruwansu da addininka ko kabilarka, matukar kai dan Arewa ne to shi kenan ka zama abokin adawa da tsangwamarsu; duk saboda takaici da jin zafin rashin mulki a hannunsu, da kuma mayar da su saniyar ware kamar yadda suke kwarmatawa. Shi ya sa suka lazumci yin bore da tayar da hakarkari don ganin sun dagulawa gwamnatocin ‘yan Arewa lissafi.
Yanzu kuma da suka ga kamar ana damawa da bangaren Yarabawa, sai suka koma suna yi musu kafar ungulu, suna neman sajewa da su don gurbata yankinsu da al’ummarsu; suna so manufar su ta tafi iri daya kafada da kafada, duk tsiyar da za su tsula a kasar nan su yi tare, ta yadda gabadaya kudancin kasar za su dunkule su zama suna magana da murya daya, shi ya sa ma ko da za a fara zanga-zangar sai suka fara ta jihar Legas inda ta fi kamari kuma ta fi tsananta da munana, dalili kuwa tsagerun kungiyoyin IPOB da MOSSOB sun shiga ciki ne ba da nufin komai ba sai da nufin raba kasa ko kuma a yi juyin juya hali kamar yadda suka fara yi fiye da shekara daya a birnin Abuja da Legas, sai dai duk da haka hakarsu ta kasa cimma ruwa, tun a wajen zanga-zangar aka samu matsala tsakaninsu da sashen Yarabawa aka raba gari.
Ya kamata tunda wuri gwamnati ta yi wa tufkar hanci, ta gargadi mutanen nan sannan ta ja wa mutanen da ke daukar nauyin duk wata zanga-zanga da za ta kawo tashin-tashina a duk sassan kasar nan. Bugu da kari kuma gwamnati ta fito fili ta ja wa shugabannin wadanan kungiyoyin nasukunnuwa, tu nuna masu cewa ba su kadai ne ba ke da korafi game da halin da kasar nan ke ciki, sa’anan kuma ba su ne kadai ke da ‘yancin fitowa su yi zanga-zangar kin amincewa da kasancewa cikin kasar nan ba, kowane bangaren kasar nan na iya yi, amma bisa lumana da kwanciyar hankali. Idan har kowa da kowa zai fito ya ce lallai sai an raba kasar ko sukar wani lamiri na gwamnati, su wane ne za su fi kwaruwa? Ai wadanda ke tinkaho ne cewa arzikin da ke warwatse a dukkan sassan kasar nan na hannunsu. To idan kuwa haka ne sai su yi la’akari da cewa mai gidan da aka yi da gilashi bai yin jifa da dutse, don kar jifarsa ta fasa masa gilashin, idan kuwa za a mayar da martani to gilasai da yawa za su ratsattsake; to su wa gari ya waya?