EndSARS: Gwamnan Gombe Ya Kaddamar Da Kwamitin Bankado Zarge-zargen Cin Zarafin Al’umma

Daga Khalid Idris Doya

Shi ma dai gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bi sahun gwamnonin Nijeriya na amsa umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar a garesu na su kafa kwamitocin musamman da za su binciko da gano irin barna da jami’an rushashshiyar tawagar jami’an ‘yan sandan SARS suka aikata na take hakkin jama’a da sauran cin zalin jama’a.

Gwamnan ya kaddamar da kwamitin ne mai mambobi 11 a jiya tare da kalubalantarsu da su maida hankali wajen yin aiki da gaskiya da adalci ba tare da nuna fifiko ko son kai ga wasu rukunin jama’an da abun ya shafa ba.

Kwamitin da aka daura wa alhakin bincikowa da bin diddidigin irin cin zarafin al’umma da jami’an suka aikata, tattaro hujjjoji, amsar korafe-korafe a rubuce ko ta hanyar bayyana a gaban kwamitin kan wannan batun da ya shafi take hakkin al’ummar.

Sauran ayyukan da aka daura wa kwamitin sun kuma hada da bincike kan dukkanin kesa-kesan cin zarafin jama’a da jami’an rushashshiyar tawagar FSARS suka aikata, baiwa gwamnati shawarorin yadda za a inganta da kyautata aikin dan sanda, gayyato shaidun da lamarin cin zarafin jama’a ya wakana a kan idonsu, gami da bada shawarorin yadda za a kiyaye faruwar irin wadannan matsalolin a nan gaba.

Kamar yadda wata kwafin sanarwar da Ismaila Uba Misili ta ce, an zakulo mambobin kwamitin ne daga hukumar kare hakkin jama’a ta Nijeriya, kungiyar matasa ta YCN, kwararru a bangaren shari’a, kungiyoyin fararen hula, dalibai, tsohon Alkalin babban kotu, Justice Sa’ad Mohammed shine shugaban kwamitin da za su gudanar da aiki a wannan kwamitin.

A jawabinsa na kaddamar da su, gwamna Inuwa Yahaya ya shaida cewa ya yi amfani da karfin ikon da doka ya ba shi na kafa irin wannan kwamitin.

Ya ce, duk da rundunar ‘yan sanda suna taka gagarumar rawa wajen kare kasa daga nau’ikan laifukan take doka da tabbatar da ‘yan kasa na bin dokoki, amma akwai bukatar yin gyaran fuskata ta wasu fannonin lura da yawaitar korafe-korafen da ake samu na take hakkin jama’a da ake zargin wasu jami’an ‘yan sanda da aikata a sassan kasar nan.

Inuwa ya ce, rushe tawagar ‘yan sandan FSARS da gwamnati ta yi abun yabo da jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, kuma hakan na nuni da yadda gwamnatin tarayya ta damu matuka da take hakkin jama’a wanda ya ce gwamnati ba za ta lamunci cigaba da hakan ba.

Ya ce rushe tawagar na daga cikin kokarin wanzar da sabon tsari da kwaskwarima wa ayyukan ‘yan sanda a kasar nan ne wanda hakan kuma zai zama abun so matuka ga ‘yan kasa.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda wasu bata gari suka kwace ragamar zanga-zangar lumana ta masu korafi kan neman a rushe SARS wanda ta rikide ta koma lalata kadarori da rasa rayuka ma a kasar nan.

Ya ce, akwai bukatar jami’an ‘yan sanda su samu ladabin mutunta jama’a da kimantasu ta hanyar da za su ke kauce wa cin zarafin jama’a a kowani lokaci.

Ya ce, shi gwamnatinsa ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyar ‘yan jihar a kowani lokaci don haka ba zai zura ido ya bar wani nau’in lamari da ke neman barazana ga lafiya da rayukan wadanda yake mulka a jihar Gombe ba.

Ya kuma ce akwai kyakkyawar hadin kai da ake samu a tsakani wajen kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar a cewarsa shugabannin addinai suna daga cikin masu bada gagaruman gudunmawa wajen tabbatuwar hakan.

Ya yi amfani da damar wajen yaba wa kokarin matasan jihar na tsame kawukansu daga biye ma wasu bata gari a sauran sassan jihohi na lalada dukiya da kadarorin jama’a da sunan zanga-zanga, yana mai cewa tabbas matasan jihar sun san abun da suke yi kuma sun cancanji jinjina.

Ya hori mambobin kwamitin da su ji tsoron Allah su gudanar da ayyukansu yadda ya dace, “Ina kira ga dukkanin wani ko wasu da jami’an rushashshiyar tawagar SARS suka keta wa haddi ko tauye wa hakki su bayyana a gaban kwamitin domin gabatar da korafinsu domin tabbatar musu da adalci.”

Kwamitin na da watanni shida da ya kammala gudanar da ayyukansa tare da gabatar da rahoton bincikensa, inda kwamitin zai ke zama a Jewel Hall, College of Nursing and Midwifery Gombe.

Shugaban kwamitin Justice Sa’ad Mohammed ya gode wa gwamnan a bisa zabinsu tare da bada tabbacinsu na yin aiki sosai bisa gaskiya da adalci ba tare da nuna son kai ba. Ya nemi dukkanin masu korafi da su bayyana a gaban kwamitin domin shigar da kokensu da ya basu tabbacin samun adalci.

Mambobin kwamitin sun hada da Honourable Justice Saad Mohammed (mai ritaya) shugaba, mambobi sun hada da tsohon kwamishinan ‘yan sanda Steben A. Anaruwa; shugaban Lauyoyi na jihar Barrister Haruna Yelma, shugaban kungiyar mata lauyoyi ta jihar Barrister, Mrs. Elizabeth Jalo-Okotie, Koodinetan kungiyar kare hakkin bil-adama a jihar Gombe Barrister Ayuba Muhammed Shamssuddeen, shugaban majalisar kungiyar matasan Nijeriya NYN a jihar Kwamared Ibrahim Mohammed.

Sauran sune: Mallam Ibrahim Yusuf da Mrs. Dudu Mamman Manuga da za su wakilci kungoyin fararen hula, shugaban kungiyar dalibai ta jihar GOSSA Aliyu Saad Hassan, Barrister Ibrahim M. Attahir, Barrister Abdulsalam Muh Kumo, yayin da kuma Barrister Caleb Ubale Shall zai zama lauyan kwamitin.

Exit mobile version