Daga Khalid Idris Doya
Kwamitin binciken cin zarafin bil adama da gwamnatin jihar Ekiti ta kafa domin binciko zarge-zargen cin zarafin da jama’an rushashshiyar tawagar SARS suka aikata, kwamitin ya amince da bada shawarar biyan diyyar naira 150,000 ga wani da rikicin EndSARS ya shafa wato Mista Adaramola Olusola.
Shugaban kwamitin, Justice Cornelius Akintayo (mai ritaya) shi ne ya bada wannan shawarar biyan diyyar a jiya yayin da ke nazartar barnar da aka yi ga motar wani mai shigar da korafi yayin zanga-zangar EndSARS.
Justice Akintayo ya lura kan cewa Mista Olusola ya gabatar da kwararan shaidu a gaban kwamitin inda ya yi zargin cewa an lalata masa motarsa kirar Peagout 505 saloon mai lamba Reg. No YEE 310 AA a yayin zanga-zangar EndSARS ta ranar 19 ga watan Oktoban 2020 da karfe 5:30 da 7:00 na yammaci a daidai layin Dalimore Junction, Ado Ekiti a inda ya ajiye motarsa domin gudanar da harkokin gabansa.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa mambobin kwamitin sun je domin ganin irin barnar da aka masa wanda wasu ‘yan daba suka aikata, inda aka farfasa masa gilan motar da wasu ababen jikinta.
“Don haka mun baiwa gwamnatin jihar shawara ta biya diyyar lalata motar da aka yi masa domin ya samu damar gyarawa. Mun bada shawarar a biya shi naira dubu dari da amshin domin ya gyara barnar da aka masa bisa adalci.”
Kwamitin ya dage zaman nasa har zuwa ranar 1 ga watan Disamban 2020