ENDSARS: Kwamitin Da Gwamnatin Legas Ta Kafa Sun Yi Mantuwa Ba Su Fadi Adadin ‘Yan Sandan Da Aka Kashe Ba -Dr. Bature Abdul’azeez

Me za ka ce dangane da rahoton kwamitin da gwmnatin Jihar Legas ta kafa kan abin da ya faru a Lekki?

Kwamitin da Jihar Legas ta kafa a kan rikicin ENDSARS, wanda ya yi babbar mantuwa, ya manta ‘yan sanda da soja sama da 70 sun rasa ransu, mtanen da ba su ji ba ba su gani ba sun wuce 100 waɗanda suka rasu, kuma mutanen da suka yi babbar asara sun haura mutum 2000, amma kwamitin da Legas ta kafa shi kawai mutum tara yake gani sun mutu a rikicin ENDSARS, baya ga mutum 200 da suka yi babbar asara a rikicin.

Ba ya duba mutum sama da 70 da suka rasa ransu da ‘yan Nijeriya sama da 100 ba su faɗa a wurin Turawan duniya sai mutanen da suka je ta da fitina su suke da haƙƙi ake zuwa ana gaya wa turawa cewa an kashe mutum tara. To mu ‘Patriotic Elders Of Nigeria’ (PEN), wato ƙungiyar masu kishin Nijeriya ina ganin an yi babban kuskure, ai da aka gayawa Turawa an kashe mutum tara, an gaya musu su ‘yan sanda ba su da ‘yanci, soja da aka kashe fiye da 70, ko ‘yan Nijeriya da da aka kashe sama da 100 ba su da ‘yanci a wajen Turawa ko a wajen Majalisar Ɗinmkin duniya.

Mu mun ce mutum tara da ake karewa ‘yanci, in ka haɗa mutum 70 kuma aka haɗa da mutum 100  su ma ‘yan Nijeriya, ji nake su ma suna da ‘yanci, masu ta da hayaniyar nan ne fa suka jawo babbar barna. Domin in za ka yi kukan an yi maka asarar mutum tara, me ya sa ba za ka yi kukan an yi asarar waɗanda suka ninka su sau 18 ba.

An kafa ƙungiyarmu domin kula da irin wannan, domin mutanen da suke zama kamar dillalan Turawa, kullum sun zama karnukan farautarsu, suna neman wani labari da za su kai musu don a baƙanta ran Afirka musamman Nijeriya, ko don a jawo wani ƙunci da tsanani a kan Nijeriya.

Wanne kira ka ke da shi ga ‘yan Nijeriya?

Ya kamata ‘yan Nijeriya mu waye mu kula da irin waɗannan mutane da ba Nijeriya suke wa aiki ba, kuma ko da akwai masu yi wa Nijeriya aiki wato Ƙunghiyoyi masu zaman kansu, kashi 95 daga cikinsu ba Nijeriya suke wa aiki ba, kashi biyar daga cikinsu ne kaɗai suke wa Nijeriya aiki, amma sauran Turawan duniya suke wa aiki.

Muna wayar da kan mutane da wannan, ka da ku yarda da yadda ake baƙantawa ƙasarku a waje, musamman kai mai karatun LEADERSHIP HAUSA, inda ma aka fi baƙantawa Arewacin Nijeriya ko kuma wani ɗan Arewacin Nijeriya. Kuma da suke fitowa suna kare haƙƙain ɗan’Adam me ya sa ba su kare haƙƙin sauran ba, me ya sa suke nema su kare haƙƙin masu haifar da fitina a ƙasa.

Wannan zanga-zanga ta ENDSARS da aka yi da gaba ɗaya sai da ta rikita Nijeriya, ai irin wannan idan aka ce an yi ta, wasu mutane kaɗan sun mutu, ai bai kamata ma a dinga wani zugugu ba domin ana ganin ƙarshen ‘yanci inda ‘yanci ba a baki yake ba babu kamar Amurka, kuna ganin yadda Trump ya riƙa kawo hargitsi dab da zai sauka a matsalisar ƙasa wanda ba don gwamnati ta yi da gaske ba, da a wannan lokaci ba a san abin da zai faru ba, amma da ya zama dole gwmanti da datse saboda al’ummar da bata ji ba bata gani ba.

Amma kai ɗan Nijeriya kai ne dillalin ɗaukar labarin cewa an kashe mutum kaza a Lekki ENSARS, to ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. ‘Yan sandan SARS suna nan kowace ƙasa su ake kira FBI, kuma akwai wasu ‘yan sandan su kuma aikin asiri suke yi sun ma fi FBI ɗin ƙarfi musamman na miyagun laifuka a ƙasa.

To haka kowace ƙasa akwai ‘yan sanda na musamman da sojoji na musamman, waɗanda sai ‘yan ta’adda na musamman suke magani. Yanzu an ce an tattara ƙararraki na mutum ko 200 ne,? to ai idan za ka tara koke-koken waɗanda abin ya shafa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a Jihar Legas ko a wasu jihohi a Nijeriya, in sun ce su 200 ne mu kuma waɗancan da abin ya shafa sun fi mutum 20,000 amma ba’a duba wannan.

Kuma me ya sa za a matsa sai an rushe SARS ɗin nan. Kai ɗan Arewa in ka duba za a ka ga ai ENDSARS ɗin ba a Arewa ta fi aiki ba, saboda duk wani laifi da ake da ya shafi cinikin ƙwaya ko satar kuɗi ta intanet duk daga can ya bullo, kuma SARS su ne a tsakaninsu suke hanawa, amma gungun waɗannan masu laifi su ne suka haɗu suka kunno wuta su da mawaƙansu waɗanda dama masu laifin ne, suka yi taro aka yi barnar da ba a taba yin ta ba.

A baya sai nake cewa ƙaiƙayi ne ya  koma kan masheƙiya, yanzu da suka zafafa aka cire SARS ɗin nan duk jihohin da aka cire su, yanzu su ne jihohin da ta’addanci yake sabo a wurinsu kamar yanzu aka fara, wanda ta’addancin dama SARS ɗin ne suka daƙile shi, yanzu ga irin halin da ake a ciki a Yamma maso Kudancin Nijeriya.

Kuma manufarsu ba ta a cire SARS ba ce nufinsu har da ‘yan sanda, ka ga idan aka cire ‘yan sanda shike nan burinsu na tabbatar da Bifara ya cika, domin duk wani haraji idan za aka biya to fa ɗan ƙungiyar Biafara za ka biya. Idan ka kula za ka ga su mutanen Gabas maso Kudu sun shiga cikin wani bala’in da ba mai iya ceton su sai Allah.

Waɗanda suka sa aka cire SARS suna dariya sai kuma suka sa aka far ma ‘yan sanda, Allah ne kaɗai ya san adadin ofisoshin ‘yan sandan da ƙona a Kudu, kuma Allah ne ya san adadin ‘yan sandan suka kwanta dama. A taƙaice dai masu zanga-zanga suka mamaye aikin da ‘yan sanda suke yi, kenan ka ga nama ya ƙare sai gidan sarkin mayu, domin waɗanda suke yankin sun shiga uku yanzu tsaronsu ya koma hannun ‘yan IPOB, sai ka ji an ce za a kwana biyu kada kowa ya fito, idan kuma ka fito ba wai tara za su yi maka ba kashe ka za su yi, in dukiya ce da kai su wawashe ta, to ina ranar korar SARS, meye fa’idar hakan.

Don haka muna yi wa Allah godiya, muna yi wa Gwamnatin Tarayya godiya, muna yi wa sojoji da ‘yan sandan Nijeriya godiya da addu’a ta musamman su ci gaba da ƙoƙarin kare Nijeriya. Ƙungiyarmu mai sun Patriotic Of Nigeria wato ƙungiyar masu kishin Nijeriya (PEN), wacce takenta Nigeria Befoe Enybody’ muna yi wa ƙasa fatan alheri.

 

Exit mobile version